Kaduna: Budurwa Ta Daɓa Wa Saurayinta Wuƙa kan Zargin Cin Amanar Soyayya

Kaduna: Budurwa Ta Daɓa Wa Saurayinta Wuƙa kan Zargin Cin Amanar Soyayya

  • Wata kotun Majistare a Kaduna ta gurfanar da Abigail Victor mai shekara 23 bisa zargin caka wa saurayinta wuka saboda zargin yaudara
  • Lauyan gwamnati ya ce Victor ta hada kai da wasu biyu da suka tsere da lakada wa Dominic James duka tare da caka masa wuka
  • Alkalin kotun ya bayar da belinta kan N200,000 da wanda zai tsaya mata, wanda dole ne ya zama cikin ‘yan uwanta da ke biyan haraji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Kotun Majistare da ke jihar Kaduna ta gurfanar da wata mata mai shekara 23 kan zargin daɓa wa saurayinta wuƙa.

Ana tsare Abigail Victor bayan caka wa Dominic James wuka saboda zargin yaudara da cin amanarta.

An tsare budurwa kan cakawa saurayinta wuka
An rufe budurwa kan daɓawa saurayinta wuƙa a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

An tsare budurwa kan jikkata saurayinta

Victor, mazauniyar Ungwan Sunday, Kaduna, ta musanta laifin hadin baki da kuma jikkata shi, wanda ake tuhumarta da su, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan gwamnati, Insifekta Chidi Leo, ya ce wacce ake zargi ta hada kai da wasu mutum biyu da ba a kama ba, suka lakada wa James duka kuma suka caka masa wuka a kafada.

Lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Mayun 2025 a Sabon Tasha, Kaduna, bayan Victor ta zargi saurayinta da yaudarta, wanda hakan ya jawo fada mai zafi.

Ya ce:

"Mai laifi ta hada kai da wasu biyu da ba a kama ba suka lakada wa saurayinta Dominic James duka, kuma suka caka masa wuka a kafada.
"Mai laifi da wanda ya shigar da kara sun samu sabani, inda ta zarge shi da yaudararta."

Lauyan ya kara da cewa mazauna unguwar ne suka shiga tsakani suka kai James asibiti domin ya samu kulawar gaggawa.

"Mutanen unguwa ne suka shiga tsakani suka taimaka masa kuma suka kai shi asibiti don samun kulawa.

- Cewar lauyan

Budurwa ta cakawa saurayinta wuka a Kaduna
An gurfanar da budurwa a kotu kan cakawa saurayinta wuka a Kaduna. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yaushe za a ci gaba da shari'ar sarauyi da budurwar?

Laifuffukan, a cewarsa, sun saba da Sashe na 58 da 284 na Kundin Laifuffuka na Jihar Kaduna, 2017, wadanda suka kunshi hukuncin daurin shekara daya zuwa biyar.

Alkalin kotu, Ibrahim Emmanuel, ya bayar da beli ga Victor da kudi N200,000 tare da wanda zai tsaya mata daidai da kudin.

Wanda zai tsaya mata sai ya kasance dan uwanta na jini kuma ya gabatar da shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku ga gwamnatin Kaduna.

"Alkalin ya bayar da belin da N200,000 da kuma wanda zai tsaya mata daidai da haka.
"Wanda zai tsaya mata dole ya kasance dan uwa na jini kuma ya gabatar da shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku ga gwamnati."

- Cewar wani jami'in kotu

Daga karshe, Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a.

Amarya ta kashe angonta a Kano

Mun ba ku labarin cewa wata amarya a Kano, Saudat Jibrin ta daba wa angonta Salisu Ibrahim wuka har lahira.

Majiyoyi sun ce an daura auren Saudat da Salisu a ranar 27 ga Afrilu, kuma amaryar ta kashe angonta a darensu na tara.

An ce Saudat ta yanka Salisu a wuya bayan ta nemi ya rufe idonsa da sunan za su yi wasa, kuma ya mutu bayan an kai shi asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.