Budurwa Ta 'Burmawa Saurayinta Wuka Har Lahira Kusa Da Dakin Hotel

Budurwa Ta 'Burmawa Saurayinta Wuka Har Lahira Kusa Da Dakin Hotel

  • Wata yarinya ta hallaka saurayinta a bayan dakin Otal cikin dare a jihar Nasarawa ranar Laraba
  • Yarinyar ta aikata wannan aika-aika ne sakamakon rashin jituwa da ya auku tsakanin masoyan
  • An garzaya da ita babban birnin jihar Lafia domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma hukunci

Lafia - Jami'an yan sanda a jihar Nasarawa sun damke wata budurwa mai suna Alice Mulak kan laifin kashe saurayinta a unguwar Mararaba dake karamar hukumar Karu ta jihar.

AIT ta ruwaito cewa Alice Mulak ta kashe saurayin ne yayinda fada ya kaure tsakaninsu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa abin ya auku ne ranar Laraba a bayan dakin Otal na City Rock Hotel.

Hoto Alice
Budurwa Ta 'Burmawa Saurayinta Wuka Har Lahira Kusa Da Dakin Hotel Hoto: @pmnews
Asali: Twitter

Ya kara da cewa tuni yarinyar ta shiga hannu kuma an gano wukan da tayi amfani da shi wajen aikata kisan.

Kara karanta wannan

Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da ya fitar yace:

"Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wannan ab ya faru ne bayan City Rock Hotel.Mararaba misalin karfe 0330hrs lokacin da mamacin da budurwarsa suke samu sabani."
"An kamata da wukan da tayi amfani da shi bisa umurnin kwamishanan yan sanda, CP Adesina Soyemi."
"An garzaya da ita sashen CID Lafia don cigaba da bincike da hukunci."

Yadda Kanin Miji Ya Kwace Matar Dan Uwansa Mai 'Ya'ya Bakwai

A wani labarin kuwa, Wani mutum mai shekaru 56 ya bayyana irin wahalar da yake sha na kula da yara bakwai da matarsa ta bar masa bayan da ta tare da kaninsa.

Simon Murefu Muyeho ya ce, kaninsa dan acaba ne, yakan dauki matarsa Farida a babur har soyayya ta kullu a tsakaninsu.

Yace, yayin da kusancinsu ya yi nisa, Farida ta bayyana soyayyarta ga kaninsa, wanda suka koma zama tare a karkashin rufi daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel