Sarkin Musulmi Ya Samo Mafita ga Gwamnatin Tarayya kan Matsalar Lantarki
- Mai alfarma Sarkin Musulmi ya taɓo batun matsalar wutar lantarkin da ake fana da ita a Najeriya ta tsawon shekaru
- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta kammala aikin madatsar ruwan Kashimbila
- Sarkin Musulmin ya nuna cewa kammala aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar lantarki a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Mai alfarma Sarkin Musulmi, AlMuhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ba gwamnatin tarayya shawara kan matsalar wutar lantarki.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kammala aikin madatsar ruwa ta Kashimbila da ke jihar Taraba.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta ce Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa aikin na da matuƙar tasiri wajen warware matsalolin wutar lantarki da ke addabar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Laraba a wajen taro kan zuba hannun jari a Taraba wanda aka gudanar a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Sarkin Musulmin ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa jajircewarsa wajen inganta tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu zuba hannun jari.
Me Sarkin Musulmi ya ce kan lantarki?
Sai dai Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda aikin madatsar ruwa ta Kashimbila ke tafiyar hawainiya, inda ya jaddada buƙatar a gaggauta kammala shi gaba ɗaya.
“Muna buƙatar wannan madatsar ruwa ta kasance a kaso 100 cikin 100. Idan da wannan aikin ya kammala kuma yana samar da wutar lantarki yanzu, da tuni mun manta da yawancin matsalolin lantarki da muke ciki yanzu."
"Gwamnatoci daban-daban sun ɗauki shekaru suna aikin, amma yanzu lokaci ne da za a mayar da hankali don a kammala shi gaba ɗaya."
"A kammala shi don ya samar da wutar lantarki ba ga Taraba kaɗai ba, har da dukkanin Arewa maso Gabas da ma ƙasa baki ɗaya."
- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi ya ce Taraba ta yi lafiya
Sarkin Musulmin ya kuma bayyana cewa Taraba ta fi samun zaman lafiya a yanzu kuma ta zama abin sha'awa ga masu zuba hannun jari, saboda irin shugabanci na gaskiya da Gwamna Kefas ke samarwa.

Asali: Facebook
“A baya, halin da ake ciki a Taraba ba mai ƙarfafa gwiwa ba ne. Amma yau, cikin ƙwarin gwiwa za mu iya cewa akwai wanda ke yin abin da ya dace. Duk yadda ka yi ƙoƙarin jawo masu zuba hannun jari, idan babu tsaro ba za su zo ba."
"Na tattauna da Gwamna Kefas, kuma na ga manyan canje-canje. Taraba yanzu ta fi samun tsaro fiye da baya, kuma mutane za su iya zuwa cikin kwanciyar lafiya."
- Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Dangote ya ba gwamnati shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshaƙin attajirin nahiyar Afirika, Alhaji Aliko Dangote, ya ba gwamnatoci shawara kan zuba hannun jari.
Aliko Dangote ya buƙaci gwamnati da ta ba da fifiko ga masu zuba hannun jari na cikin gida domin bunƙasa tattalin arziƙi.
Dangote ya nuna cewa hakan na da muhimmanci domin sai akwai masu zuba hannun jari na cikin gida sannan na waje za su shigo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng