Kyautar N5m ga Wanda Ya Gano Fursunoni 7 da Suka Tsere daga Osun, An Saki hotuna

Kyautar N5m ga Wanda Ya Gano Fursunoni 7 da Suka Tsere daga Osun, An Saki hotuna

  • Hukumar gidajen gyaran hali ta sanya kyautar Naira miliyan 5 ga duk wanda ya bada bayanai kan fursunonin da suka tsere a Osun
  • Jami’an tsaro sun hada kai da NCoS domin cafke fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan gyara hali na Ilesa yayin ruwan sama
  • Hukumar ta bayyana hanyoyin tuntuɓa da ta samar don sauƙaƙa isar da bayanai, tare da tabbatar da ba da kariya ga masu kwarmato

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta sanya kyautar Naira miliyan 5 ga duk wanda ya bada sahihan bayanai kan fursunonin da suka tsere a Osun.

A safiyar ranar Laraba ne Legit Hausa ta rahoto cewa fursunoni bakwai sun tsere daga gidan gyaran hali na Ilesa da ke Osun ana tsakiyar ruwan sama.

Gwamnati ta sanya kyautar N5m ga wanda ya bayar da bayanai a kan fursunoni 7 da suka tsere a Osun
Hukumar gidajen yari ta fitar da hotuna da bayanan fursunoni 7 da suka tsere a Osun. Hoto: @CorrectionsNg
Asali: Twitter

Gwamnati ta tsananta farautar fursunoni 7

Jami'in hulda da jama'a na hukumar gyaran hali, Umar Abubakar, ya fitar da sanarwar sanya kyautar kudin a shafin NCoS na X a yammacin yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Umar Abubakar na zuwa ne awanni bayan da hukumar ta tabbatar da cewa ta hada kai da sauran jami'an tsaro domin cafko fursunonin da suka gudu.

Hukumar NCoS ta bukaci 'yan Najeriya da su taimaka mata ta hanyar bayar da duk wata amintacciyar masaniya game da fursunonin bakwai.

Sanarwar mai magana da yawun hukumar ta ce mutane na iya kai irin wannan rahoto kai tsaye ga ofishin hukumar tsaro mafi kusa ko a kira ta a lambobinta.

Gwamnati ta sanya kyautar N5m

Hukumar ta tabbatar cewa za ta kiyaye bayanan duk wanda ya kawo mata kwarmaton inda za a iya kama wadannan fursunonin.

Sannan hukumar ta ce za ta yi amfani da bayanan da mutane suka bayar domin ganin wadanda suka tsere ba su sake aikata wani laifin a cikin al'umma ba.

Baya ga boye bayanan masu kwarmato, hukumar ta kuma ce akwai kyautar Naira miliyan 5 ga duk fursuna daya da aka bayar da masaniyar inda za a kama shi.

An kuma gargadi 'yan kasar da kada su taimaka wa masu laifin ta hanyar boye su, wanda hakan laifi ne, yayin da ta ce kai rahotonsu ga jami'an tsaro ne ya fi dacewa.

Sunaye da adireshin fursunonin da suka tsere

Sanarwar Umar na hade da hotunan fursunonin bakwai da suka tsere, sunayensu da kuma adireshinsu kamar haka:

  • John Micheal

Shekaru: 34

Adireshi: Emene, jihar Enugu

  • Tobi Akin

Shekaru: 19

Adireshi: Gaban makarantar DC, Oke Ejigbo, jihar Osun

  • Eze Nweze

Shekaru: 40

Adireshi: Gida mai lamba 26, titin Ayegbajeje, Ikorodu, jihar Legas

  • Ninalowo Yusuf

Shekaru: 28

Adireshi: Gida mai lamba 1, Idowu close, Ojo, jihar Legas

  • Olakejab Ajofoyinbo

ShekaruL 45

Adireshi: Ilupeju, jihar Ekiti

  • Mattew Ogunjimi

Shekaru: 20

Adireshi: Lamba 53, titin Owode, Ikirun, jihar Osun

  • Kabiru Oyedun

Shekaru: 39

Adireshi: Gida mai lamba 56, Orita Agunla, Omu, jihar Legas

Hukumar gidajen yari suns aki hotuna da bayanan fursunoni 7 da suka tsere a Osun
Shugaban hukumar gidajen yari ta Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche tare da mukarrabansa. Hoto: @CorrectionsNg
Asali: Twitter

Hanyoyin tuntubar hukumar gidajen yari

Domin saukaka tuntubar hukumar yayin da aka samu bayanai kan fursunonin, an samar da hanyoyin sadarwa na musamman.

Wadannan hanyoyin sun hada da aika bayani ta adireshin imel, complaintresponsedesk@corrections.gov.ng da kuma info@corrections.gov.ng.

Hakazalika, hukumar ta kuma bayar da lambobin waya kamar haka: 07087086005, 09060004598, da 08075050006.

Hukumar ta nanata cewa hadin kan jama’a yana da matukar muhimmanci don dawo da tsaro da kama wadanda suka tsere.

Duba hotunan wadanda suka tsere a kasa:

Fursunoni 12 sun tsere daga gidan yarin Kogi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a safiyar Litinin, 24 ga Maris, 2025, fursunoni 12 sun tsere daga gidan gyaran hali na tarayya da ke Kotonkarfe, jihar Kogi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce abin mamaki ne yadda fursunonin suka gudu ba tare da sun lalata wani abu ba.

Ya kuma tabbatar wa jama’ar Kogi da ‘yan Najeriya cewa gwamnati da hukumomin tsaro za su ɗauki matakai don hana maimaituwar lamarin nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.