Fursunoni 7 Sun Faki Idon Jami'ai, Sun Tsere daga Gidan Yari Ana Sheka Ruwan Sama
- Fursunoni bakwai sun tsere daga gidan gyaran hali na Ilesa, jihar Osun, bayan ruwan sama mai ƙarfi ya rushe bangon da ke kewaye da gidan
- Hukumar gyaran hali ta ce tana binciken lamarin tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin kamo fursunonin da suka tsere
- Wannan ba shi ne karo na farko da hakan ke faruwa ba, domin a 2024 an samu irin wannan tserewa a Maiduguri bayan madatsar ruwa ta fashe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun – Fursunoni bakwai sun tsere daga gidan gyaran hali (MSCC) da ke Ilesa, jihar Osun, bayan ruwan sama mai karfi ya rushe ginin bangon wajen.
Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da faruwar lamarin, inda aka ce fursunonin sun tsere da misalin ƙarfe 2:00 na daren Talata, a yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi.

Asali: Twitter
An fara farautar fursunoni 7 da suka tsere a Osun
A daren ranar Talata, mai magana da yawun NCoS, Umar Abubakar, fitar da sanarwa a shafin hukumar na X cewar ana ci gaba da bincike da kuma farautar waɗanda suka tsere.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa shugaban hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi don gano kura-kuran tsaro da suka janyo lamarin.
NCoS na aiki tare da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin gano inda fursunonin suka shiga, kamar yadda Umar Abubakar ya bayyana.
Ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani bayani da zai taimaka ta layukan wayar hukumar kamar haka: 07087086005, 09060004598 da 08075050006.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ba a bayyana sunaye da laifukan fursunonin da suka tsere ba a lokacin fitar da wannan rahoto.
Daruruwan fursunoni sun tsere a Maiduguri
An taba samun irin haka a Maiduguri, jihar Borno a ranar 10 ga Satumba, 2024, inda ambaliya daga rushewar madatsar ruwa ta Alau ta rusa bangon gidan yarin garin.
A wancan lokaci, NCoS ta tabbatar da cewa daruruwan fursunoni ne suka tsere, sai dai guda bakwai ne aka sake kama su zuwa 15 ga Satumba, 2024, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
An gano cewa akwai shugabannin Boko Haram a cikin fursunonin da suka tsere a Maiduguri, wanda hakan ya sa aka dauki matakan tsaro na gaggawa, tare da sakin bayanan su don sauƙaƙe kamo su.

Asali: Twitter
Tserewar fursunoni a gidan yarin Delta
A baya, a watan Afrilu 2022, wasu fursunoni sun tsere daga gidan gyaran hali na Agbor da ke jihar Delta, bayan ruwan sama ya taru a gefen bango, har ya rushe ginin.
Mun ruwaito cewa ruwa ya kwanta a jikin bangon na tsawon lokaci bayan ruwan sama ya tsaya, lamarin da ya janyo rushewar bangon.
Umar Abubakar ya ce hukumar za ta kara tsaurara matakan tsaro a gidan yarin Ilesa da sauran gidajen yari yayin da ake ci gaba da farautar wadanda suka tsere.
Fursunoni 12 sun tsere a gidan yarin Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla fursunoni 12 ne suka tsere daga gidan gyaran hali da tarbiyya na Kotonkarfe, da ke a jihar Kogi.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Kingsley Fanwo, ya ce abin mamaki ne ganin yadda fursunonin suka gudu ba tare da wata alamar lalata gini ba.
Ya bayyana cewa Gwamna Usman Ododo ya riga ya bayar da umarni na gaggawa don cafko wadanda suka tsere, tare da ƙarfafa tsaro a gidan yarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng