Tinubu Ya Jawo Magana wajen Babban Kirista kan Ganawa da Fafaroma Leo
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana ganawar Bola Tinubu da Fafaroma a matsayin raini ga Kiristoci
- Babachir Lawal ya ce halartar shugaba Tinubu wajen bikin nadin Fafaroma Leo XIV ba wani gagarumin abin alfahari ba ne
- Babachir ya kara jaddada cewa tikitin Musulmi da Musulmi da Tinubu ya lashe zabe da shi rashin adalci ne ga Kiristoci a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya yi kaca-kaca da ganawar Shugaba Bola Tinubu da sabon Fafaroma Leo XIV a birnin Vatican.
Babachir Lawal ya yi magana yana mai cewa hakan wani lamari ne da ya nuna raini ga Kiristoci a Najeriya.

Asali: Facebook
Ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, ya ce ba wani abin alfahari ba ne shugaban kasa ya halarci bikin nadin Fafaroma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa, da akwai mataimaki Kirista a matsayin mataimakin shugaban kasa, da shi ne ya dace ya wakilci Najeriya wajen irin wannan muhimmin biki na addini.
Babachir ya soki ganawar Tinubu da Fafaroma
Babachir Lawal ya ce ganawar da Tinubu ya yi da Fafaroma ba wani babban ci gaba ba ne, ya ce ana iya samun irin wannan gayyata ta hanyoyin siyasa da kuma kulla hulda.
Vanguard ta wallafa cewa Babachir ya ce:
"Ba wani gagarumin lamari ba ne ganin shugaban kasa yana ganawa da Fafaroma. Ana iya hada irin wannar ganawar ta wasu hanyoyi.
"Don haka wannan ganawa ba wani abin ban mamaki ba ne,"
Babachir ya ce bai kamata Tinubu ya jagoranci wakilan Kiristoci zuwa Vatican ba, yana mai cewa hakan na nuna rashin adalci da aka yi wa Kiristoci ta hanyar tsarin tikitin Musulmi da Musulmi.
Babachir ya soki tikitin Muslim Muslim
Babachir Lawal ya kara jaddada cewa tsarin tsayar da Musulmi biyu a matsayin shugaban kasa da mataimaki bai dace ba a kasa mai yawan Kiristoci kamar Najeriya.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Wannan lamari ya tabbatar da ra’ayina tun farko cewa tsarin Musulmi da Musulmi raini ne ga Kiristoci.
"Da akwai mataimaki Kirista, shi ne ya kamata ya wakilci gwamnati a wajen wannan biki. Amma yanzu Musulmi ne ke jagorantar tawagar Kiristoci zuwa Vatican.”
A lokacin shirye-shiryen zaben 2023, Babachir Lawal na daga cikin wadanda suka fara goyon bayan Tinubu.
Sai dai Babachir ya janye goyon bayansa bayan Tinubu ya zabi Kashim Shettima, wanda shi ma Musulmi ne, a matsayin abokin takararsa.
Legit ta tattauna da malamin addini
Wani malamin addini a jihar Taraba, Muhammad Abubakar ya zantawa Legit cewa abin da Tinubu ya yi ba koyarwar addinin Musulunci ba ne.
Malamin ya ce:
"Ba laifi ba ne ya musu jaje, amma yin tarayya da su wajen ibada ba koyarwar Musulunci ba ne. Abin da ya fi shi ne ya tura wakilai Kiristoci."
Musulman shugabanni da suka je nada Fafaroma
A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya wuce aka yi bikin nada sabon Fafaroma a fadar Vatican da ke Roma a kasar Italiya.
Shugabannin kasashen duniya sama da 30 ne suka halarci bikin nada sabon Fafaroman, wanda shi ne dan kasar Amurka na farko da ya rike babban matsayin a tarihi.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na cikin jerin Musulman shugabanni a fadin duniya da suka halarci nadin Fafaroma Leo a Vatican.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng