Oyo: 'Yan Majalisa 2 Sun Fusata da Majalisar Dokoki Ta Canza Shawara kan Dokar Sarauta

Oyo: 'Yan Majalisa 2 Sun Fusata da Majalisar Dokoki Ta Canza Shawara kan Dokar Sarauta

  • Bayan shan matsin lamba, Majalisar Dokokin Oyo ta gyara dokar sarauta da ta maida Alaafin na jihar shugaban majalisar sarakuna na dindindin
  • Majalisar ta gyara dokar ne a zamanta na jiya Talata, 20 ga watan Mayu bayan karɓar rahoton kwamitin kananan hukumomi da masarautu
  • Sai dai wannan mataki bai yi wa ƴan Majalisa biyu daɗi ba kuma an ruwaito cewa ba su bari an gama zaman ba suka fice daga zauren Majalisar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta yi amai ta lashe kan kudirin dokar sarauta da ta amince da ita a kwanakin baya.

Majalisar Dokokin ta sauya shawara, ta gyaran dokar sarauta da ta kunshi mayar da Alaafin na Oyo a matsayin shugaban Majalisar Sarakuna da Masarautun Oyo na dindindin.

Majalisar Dokokin Oyo.
Majalisar dokokin jihar Oyo ya gyara dokar sarauta kan shugabancin majalisar sarakuna Hoto: @Adebo_Ogund
Asali: Twitter

Jaridar Tribune Nigeria ta tataro cewa Majalisar ta gyara dokar ne bayan ta karɓi rahoto daga kwamitin majalisa mai kula da harkokin ƙananan hukumomi da masarautu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta canza dokar sarauta a Oyo

Bayan tafka muhawara kan rahoton, majalisar ta yanke cewa shugabancin majalisar sarakunan ya rika juyawa tsakanin Alaafin na Oyo, Olubadan na Ibadanland, da kuma Soun na Ogbomosoland.

Wannan na nufin daga yanzu manyan sarakunan guda uku za su riƙa karɓa-karɓa na shugabancin Majalisar Sarakunan Oyo.

Majalisar ta amince da kudirin gyaran dokar ne bayan karatu na uku da aka yi masa a zamanta na ranar Talata, 20 ga watan Mayu, 2025.

Haka kuma, ‘yan majalisar sun amince da nadin shugabanni 13 na majalisar sarakunan jihar Oyo, ciki har da Otun da Osi Olubadan na Ibadanland.

Mambobi 2 sun fusata sun fita daga Majalisa

Sai dai wannan matsaya ta Majalisar ba ta yi wa ‘yan majalisa daga mazaɓun Oyo ta Gabas da Atiba, Hon. Olorunpoto Rahman da Hon. Gbenga Oyekola, dadi ba.

Dukkaninsu sun fice daga zauren majalisar a lokacin da ake tattaunawa kan rahoton kwamitin, kamar yadda Punch ta rahoto.

A wata hira da Hon. Rahman ya yi da manema labarai, ya ce,

"Ya kamata a dogara da gaskiya wajen yin kowace doka. Kowa ya san matsayin Alaafin, ba mu manta da tarihi ba.
“Alaafin sarauta ce mafi girma. Kada mu rika yin dokoki saboda dalilan siyasa kawai, ya kamata mu kirkiri doka da za ta dawwama, wadda za ta yi daidai da tarihi.”
Alaafin na Oyo.
Yan majalisa sun tuna ƙimar Alaafin na Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Ya ci gaba da cewa;

“Ba mu gamsu da yadda kwamitin ya yi aikinsa ba. Ba a gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a ko na masu ruwa da tsaki ba.
"Babu wani lokaci da suka gayyaci kowa daga Oyo domin ya ba da ra’ayinsa game da kudirin. Ina da matsala sosai da wannan.”

Matsayin sarkin Sasa a dokar jihar Oyo

A wani labarin, kun ji cewa mai martaba Olubadan na ƙasar Ibadan a jihar Oyo, Owolabi Olakulehin ya yi ƙarin haske kan sarautar sarkin Sasa.

Olubadan ya bayyana cewa a hukumance, doka ba ta ba sarkin Sasa ikon wakiltar Olubadan ba kamar yadda ake tunani.

Basaraken ya bayyana cewa Cif Akinade Ajani Amusa shi ne Baale na Sasa, kuma wakilin hukuma na masarautar Ibadan a yankin Sasa

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262