Sule Lamido: 'Yadda na Kwantar da Tarzoma tsakanin 'Yar'Adua da Obasanjo'

Sule Lamido: 'Yadda na Kwantar da Tarzoma tsakanin 'Yar'Adua da Obasanjo'

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya bayyana yadda ya shiga tsakani wajen kwantar tarzoma tsakanin tsofaffin shugabannin Najeriya biyu
  • A cikin littafin tarihin rayuwarsa, Sule ya ce wasu batutuwa sun taso a kan samar da wutar lantarki da gwamnatin Olusegun Obasanjo ta dauko
  • Ya fadi yadda Umaru Musa 'Yar'Adua ya shaida masa gatan da ya shimfidawa Obasanjo a gwamnatinsa lokacin da ake tsoron yana bincikensa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaSule Lamido, ya bayyana abubuwan da suka faru kafin ya yanke shawarar roƙon marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa 'Yar’Adua da kada ya yi rigima da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.

A shafuka na 257 da 258 na littafin tarihin rayuwarsa da ya wallafa, Sule Lamido ya tuna wasu abubuwa da suka so jawo sabani a tsakanin tsofaffin shugabannin biyu.

Lamido
Sule Lamido ya ce ya kwantar da rikici tsakanin Obasanji da Yar'Adua Hoto: Sule Lamido
Asali: Facebook

Vanguard News, tsohon gwamnan ya ja hankalin marigayi Yar’Adua kan wata muhawara da ‘yan Majalisar Wakilai suka yi kan shirin samar da wutar lantarki da gwamnatin Obasanjo ta fara a kan $16m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Sule Lamido ya fadawa Yar’Adua

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Sule Lamido ya bayyana cewa ya yiwa shugaban Najeriya a wancan lokaci, Umaru Musa 'Yar'Adua kan batun Obasanjo a majalisa.

Obasanjo
Sule Lamido ya ce an yi dambarwa kan kudin samar da lantarki na gwamnatin Obasanjo Hoto: Hoto: Olusegun Obasanjo Quotes
Asali: Facebook

Ya ce:

“Da ace ‘yan adawa ne suka jagoranci wannan muhawara a Majalisar Wakilai, da hakan ba abin mamaki ba ne. Amma abin mamaki shi ne jagoran muhawarar babban jigo ne na jam’iyyar PDP daga jihar Katsina, kuma aboki na kusa da Shugaba Yar’Adua.”
“Yadda ake gabatar da batun a gaban ‘yan Najeriya ya nuna kamar Obasanjo ne ya wawure dala biliyan 16, amma daga baya an gano akasin hakan.”
“Na tafi wajen Shugaba Yar’Adua na ja hankalinsa kan wannan muhawara da ake yi a Majalisar Wakilai kan batun wutar lantarki. Sai ya ce da ni ai wannan magana ce da wata rashen gwamnati mai zaman kanta ke tattaunawa akai.’”

Sule Lamido ya roki Yar’Adua

Tsohon gwamnan ya ce ya tunatar da dukkan ma’aikatan fadar shugaban kasa cewa da ba don Obasanjo ba, da Yar’Adua zai zama shugaban ƙasa ba.

Ya ce bayan ya yi wannan bayani ne kuma sai ya karasa wajen marigayi 'Yar'Adua domin ya shaida masa abin da ke ci masa tuwo a kwarya.

Yayin da ya isa kusa da teburin shugaban, tsohon gwamnan ya ce sai marigayi Yar’Adua tambaye shi ko akwai abin da ke damunsa.

Sule ya ce:

“Na kusan durƙusawa cikin hawaye na ce masa: ‘Don Allah, kada ka yi fada da Obasanjo.
“Sai ya ce min, ‘Sule, ka nutsu. Ka zauna.’ Nan take ya kira hadiminsa, Laftanar Kanal Mustapha. Da ya shigo, sai shugaban ƙasa ya tambaye shi kai tsaye: ‘ADC, mene ne umarnin da na baka game da Obasanjo?’”
“ADC ya amsa da cewa: ‘Ranka ya daɗe, ka umarce ni da in amince da duk wata buƙata da ta shafi Obasanjo, ko a ciki ko wajen Najeriya, har da tafiyarsa, ba tare da na nemi izinin ka ba.’”

Bayan ya ji wannan ne sai hankalinsa ya kwanta, kafin nan kuwa Sule ya yi kaca-kaca da babban dogarin Marigayi Yar'adua.

Sule Lamido ya ci gyaran IBB

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa dalilin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), ya bayar kan soke zaɓen 1993.

Lamido ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa, inda ya ce hujjar da Babangida ya bayar shi ne Moshood Abiola yana bin Najeriya bashin Naira biliyan 45.

Wannan magana ta fito ne a daidai lokacin da al’umma ke ci gaba da nazari kan zaɓen 1993, wanda ganin cewa ana samun dalilai daban-daban a kan soke zaben da MKO ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.