Duk da Rikicin Masarauta, Sarki Sanusi II Ya Sake Nadin Sarauta a Kano

Duk da Rikicin Masarauta, Sarki Sanusi II Ya Sake Nadin Sarauta a Kano

  • Duk da jiran shari'a a Kotun koli, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sake yin nadin sabuwar sarauta a jihar Kano
  • Sanusi II ya naɗa Alhaji Bashir Yusuf Madaki a matsayin sabon Dagacin garin Kenfawa da ke cikin Garun Mallam
  • Sanarwar da aka wallafa a shafin Sanusi II Dynasty ta bayyana hakan da daren ranar Laraba, 30 ga watan Afrilu, 2025
  • A cewar sanarwar, an nada dagacin ne domin tabbatar da shugabanci mai inganci da ci gaba da tafiyar da harkokin gargajiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake yin nadin sarauta a jihar duk da dakon hukuncin kotu da ake yi.

Mai Martaba Sanusi II ya naɗa sabon dagaci a garin Kenfawa da ke karamar hukumar Garun Mallam a jihar Kano.

Sarki Sanusi II ya naɗa sabon dagaci a Kano
Sarki Sanusi II ya kuma nada sabon dagaci a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a manhajar Facebook a daren yau Laraba 30 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II zai yi bikin nadin Yariman Kano

Wannan na zuwa ne bayan basaraken ya sanar da cewa za a gudanar da nadin sabon Yariman Kano, Alhaji Ahmed Abbas Sanusi a jihar.

Rahotanni suka ce za a bikin ne a fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar Juma’a mai zuwa 2 ga watan Afrilun 2025.

An ruwaito cewa sabon Yariman Kano ya kasance Wakilin Marigayi Galadima, wanda ya rasu kwanan nan bayan jinya.

Hakan na zuwa ne bayan sarki Muhammadu Sanusi II ya yi sababbin nade-nade da sauye-sauye a majalisar masarautar Kano.

Masarautar Kano: Har yanzu ana jiran hukuncin kotu

Dukan wadannan nade-naden na zuwa ne yayin rigimar sarauta a Kano ba ta kawo ƙarshe ba saboda dakon hukuncin kotu.

Har yanzu ana ci gaba da jiran hukuncin ƙarshe daga Kotun Koli bayan hukunce-hukuncen da kotuna da dama suka yanke a baya.

Sanusi II ya ci gaba da nadin sarauta a Kano
Sarki Sanusi II ya kuma nadin sabon dagaci a karamar hukumar Garum Mallam. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Sanusi II ya naɗa sabon dagaci a Kano

Sanarwar ta ce sabon dagacin mai suna Alh. Bashir Yusuf Madaki zai fara aiki nan take a garinsa da ke Kenfawa.

Rahotanni suka ce basaraken ya ba da muƙamin ne domin ci gaba da gudanar da shugabanci mai inganci.

Sanarwar ta ce:

"Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi ll CON, ya nada Alh. Bashir Yusuf Madaki sarauta a Kano.
"An nada Bashir Yusuf Mafarki ne a matsayin sabon Dagacin garin Kenfawa da ke karamar hukumar Garun Mallam."

Aminu Ado Bayero ya nada sabon Galadiman Kano

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ɗaga darajar sarautar yayansa Alhaji Sanusi Ado Bayero daga Wamban Kano.

Aminu Ado ya naɗa Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano bayan taron majalisar masarautar Kano bayan Sarki Sanusi II shi ma ya nada na shi.

Naɗin na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi wanda ya rasu bayan ya yi fama da jinya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.