Bayan APC Ta Dakardar da Shi, Ɗan Majalisar Tarayya Na Fuskantar Kiranye Daga Mazaɓarsa

Bayan APC Ta Dakardar da Shi, Ɗan Majalisar Tarayya Na Fuskantar Kiranye Daga Mazaɓarsa

  • Yayin da jam'iyyar APC da dakatar da ɗan Majalisar Tarayya a jihar Zamfara, Aminu Sani Jaji ya sake shiga wata matsala
  • Jama'ar yankin mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji sun yi korafi kan yadda mamban ke wakiltarsu ba tare da kulawa ba
  • Legit Hausa ta tattauna da daya daga cikin wakilan Hon. Aminu Sani Jaji kan wannan shiri da ake yi a mazaɓarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Ƴan mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara sun fara shirin kiranye kan ɗan Majalisar Tarayya a yankin, Aminu Sani Jaji.

Jama'ar yankin suka ce sun yi nadamar zaben Jaji shiyasa suke kokarin daukar wannan mataki a kansa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: EFCC za ta binciki 'dan majalisa kan daukan nauyin ta'addanci

Dan Majalisar Tarayya daga APC na fuskantar kiranye daga mazabarsa
Aminu Sani Jaji na fuskantar kiranye bayan APC ta dakatar da shi. Hoto: @Aminu_Jaji.
Asali: Twitter

Ana shirin kiranye kan ɗan Majalisar APC

Jaji shi ke wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gamayyar kungiyoyi suka fitar da ke mazabar kan dan Majalisar.

Kungiyar ta ce daukar wannan mataki kan Jaji ya dace da sashe na 69 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, TheCable ta tattaro.

Shugaban gamayyar Coalition for Sustainable Development, Bello Mahmud shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa, cewar rahoton Vanguard.

Musabbabin kiranye kan Sani Jaji na APC

Mahmud ya ce za a iya yiwa ɗan Majalisa kiranye idan fiye da rabin masu zabe suka sanya hannun amincewa da haka aka gabatar ga hukumar zabe.

Ya ce sun yi nadamar zabensa kuma basu da wani buri a kansa saboda yadda yake wakiltar yankin a Majalisa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar Zamfara

Matashin ya ce sun bukaci takardun da za su cike daga hukumar zabe na kiranye kan Jaji ba da ba ta lokaci ba.

Har ila yau, ya ce yankin na daga cikin wadanda ke fama da hare-haren 'yan bindiga amma Jaji bai taba ziyartarsu ba kan halin da suke ciki.

Ya ce kuma Jaji bai taba kawo wani tallafi ga jama'ar yankin ba duk da irin halin da suka fada a ciki.

Legit Hausa ta tattauna da wakilin Hon. Jaji

Legit Hausa ta tattauna da daya daga cikin wakilan Hon. Aminu Sani Jaji kan wannan shiri da ake yi.

Hon. Mansur Khalifa ya ce wadannan biyansu aka yi domin su batawa Jaji suna amma babu wani korafi da ƴan mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji ke yi.

Khalifa wanda tsohon Kwamishina ne kuma tsohon hadimi na musamman ya ce su wadanda suka shirya wannan abu ko yawan mazabun yankin basu sani ba.

Kara karanta wannan

Niger: Ministar Tinubu ta yi amai ta lashe, ta dauki mataki kan aurar da mata 100

"Wannan ƙungiya babu wanda ya fito daga Zamfara ta Arewa, suna zaune ne a Abuja su wanke shadda su yi turanci a daura musu abin daukar hoto."
"Daukar nauyinsu aka yi, ko wanda suka yi wa aiki zasu iya cin amanarsa idan ya biya su saboda haka daukar nauyinsu aka yi."
"Maganar rashin jaje ko tallafi kuwa, wannan karya ne saboda ina daga cikin wakilan da ke aika dukkan sakon Jaji ga jama'ar yankinsa, babu wani rasuwa da za a yi da Hon. bai je ya yi jaje ba da kuma tura kudi da buhun shinkafa."

- Mansur Khalifa

Har ila yau, Khalifa ya ce maganar dakatar da Jaji a APC maganar banza ce kawai wasu ne ke haddasa da yadda Jaji ke gudanar da shugabancinsa ya tsole musu ido shi ne suke son shafa masa kashin kaji.

APC ta dakatar da ɗan Majalisar Tarayya

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta dakatar da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Jam'iyyar ta dauki wannan mataki ne kan Sani Jaji saboda zargin cin dunduniyarta a zaben 2023 da aka gudanar

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.