Bincike Ya Bankado Dalilin Ragargajewar Farashin Buhun Shinkafa a Najeriya

Bincike Ya Bankado Dalilin Ragargajewar Farashin Buhun Shinkafa a Najeriya

  • Farashin buhun shinkafa mai kilo 50 ya sauka daga N80,000 zuwa N58,000 a wasu sassan Najeriya saboda shigo da na waje
  • Indiya ta fitar da tan miliyan 5.35 na shinkafa zuwa Yammacin Afirka a 2024, wanda ya cika ɗakunan ajiya a kasar Benin
  • Duk da faduwar farashin, mutane ba sa yawan sayen shinkafa yadda ake sa rai, suna jiran farashin ya kara karye wa sosai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu sassan Najeriya, musamman a yankunan karkara bayan shigo da ita daga kasar Benin.

Wani rahoto daga S&P Global, wata ƙungiya ta ƙwararrun masana harkar noma, ya bayyana cewa kasuwar shinkafa a yankin Yammacin Afrika ta fuskanci koma baya a cikin shekaru biyu.

Hatsi
Farashin shinkafa ya karye Hoto: Ramalan Haruna
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan yadda kayayyaki ke cika kasuwannin yankin sakamakon cire harajin fitar da shinkafa da gwamnatin Indiya ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu saukin farashin shinkafa

Rahoton Platts, wani bangare na S&P Global Commodity, ya bayyana cewa yawan shinkafa mai arha da ke zuwa daga Indiya ya cika manyan ɗakunan ajiya na Benin. Daga watan Satumba zuwa Disamba, rahotanni sun nuna cewa Indiya ta fitar da kusan tan miliyan 2.11 na shinkafa zuwa Yammacin Afirka.

Rahoton ya kara da cewa wannan adadi ya ninka ninki fiye da tan 720,000 da aka fitar a shekarar 2023, lamarin da ya jawo karyewar farashi.

Shinkafar Indiya ta cika kasuwannin Najeriya

Rahoton ya kara da cewa a shekarar 2024 gaba ɗaya, Indiya ta fitar da tan miliyan 5.35 na shinkafa zuwa Yammacin Afrika, idan aka kwatanta da tan miliyan 3.9 da aka samu a 2023.

Hatsi
Kasuwar hatsi a Najeriya Hoto: Ramalan Haruna
Asali: UGC

Wani ɗan kasuwa da ke zaune a Togo ya bayyana cewa halin da ake ciki a kusan dukkan yankunan Yammacin Afrika iri ɗaya ne — ba ciniki a kasuwa, kuma farashi yana raguwa. Yayin da Najeriya, wacce ita ce babbar kasuwar shinkafa ga Benin, ke ci gaba da shigo da shinkafa ta barauniyar hanya, farashin shinkafar gida da waje ya karye.

Jama'a ba sa iya sayen buhun shinkafa

Rahotanni sun bayyana cewa farashin buhun shinkafa na gida mai kilo 50 ya fadi daga tsakanin N80,000 da N90,000, zuwa N60,000, yayin da farashin shinkafa daga Indiya ya sauka zuwa N80,000.

Wani ɗan kasuwa ya ce:

"Duk da saukin farashi, buƙatar shinkafa ba ta karu yadda ake tsammani ba. Saboda yadda farashi ke ci gaba da sauka kullum."
"Masu saye suna jinkiri suna jiran farashin ya daidaita kafin su fara sayayya."

Dalilin rage sayen shinkafa a Najeriya

Wasu daga cikin mutanen da suka tattauna da Legit sun ce ba sa iya sayen shinkafa saboda har yanzu tana da tsada sosai.

Wani magidanci mai suna Muhammad ya ce:

"Kudin da nake samu ba zai isa na sayi buhun shinkafa da sauran kayan abinci ba. Dole sai na sayi kwano uku ko hudu, sai in dafa da sauran kayan abinci." Malama Jamila ta bayyana cewa:
"Ai yanzu a garin nan ba kudi. Ko nawa aka ba ka, ba zai isa ka je kasuwa ka sayi buhun shinkafa ba; sai dai ka auna kadan kadan."

Salamatu ta ce:

"Ai yanzu mun saba cin har tuwon dawa tun bayan da shinkafa ta yi tsada. Masara da sauran kayan tuwo sun fi rike ciki, shi ya sa muke fi sayensu a kan shinkafa."

Farashin hatsi ya ragu a Najeriya

A baya, mun ruwaito cewa an samu ragin farashin kayan abinci a kasuwar hatsi ta karamar hukumar Potiskum da ke jihar Yobe, lamarin da ya faranta wa talakawan kasar nan.

A yayin da wasu farashin abinci suka sauka, rahotanni sun nuna cewa farashin wake ya tashi, yayin da ake sayar da buhun shinkafa mai aure kan N51,000 a yanzu.

Hakazalika, rahoton ya nuna cewa farashin buhun dawa ‘yar Kaura ya koma N41,000 zuwa N43,000, yayin da dawa fara ta koma tsakanin N36,000 zuwa N37,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.