Gwamantin Tarayya Ta Fadi Ribar da aka Fara Samu saboda Tsare Tsaren Tinubu

Gwamantin Tarayya Ta Fadi Ribar da aka Fara Samu saboda Tsare Tsaren Tinubu

  • Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da da mai ido
  • Ya ce bayanai daga Cibiyar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa hauhawar farashin kaya ya ragu daga 24.23% zuwa 23.71% a watan Afrilun 2025
  • Ministan ya ce saukar hauhawar farashin ya samo asali ne daga raguwar farashin abinci kamar shinkafa, wake, masara da dawa da aka samu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce alamu na nuna cewa manufofin tattalin arzikin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da ɗa mai ido.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai karo na takwas da aka gudanar a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a.

Mohammed Idris
Ministan yada labarai ya ce tsare tsaren Tinubu sun fara aiki. Hoto: Federal Ministry of Information
Asali: Twitter

The Cable ta wallafa cewa Mohammed Idris ya bayyana cewa bayanai daga Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa hauhawar farashi ya ragu a watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin cewa an samu sauki a mulkin Tinubu

Ministan ya bayyana cewa saukar farashin na nuna cewa matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun fara tasiri.

Mohammed Idris ya ce:

“A yau, ina farin cikin sanar da al’umma cewa Cibiyar Kididdiga ta Ƙasa ta fitar da sababbin bayanai kan tasirin hauhawar farashi a watan Afrilu.
"An samu ragin 0.52% daga 24.23% da aka samu a watan Maris zuwa 23.71% a watan Afrilu.”

Punch ta wallafa cewa ministan a ƙara da cewa:

“Haka kuma, idan aka duba matakin wata-wata, hauhawar farashi ya ragu da kashi 2.04%, daga 3.90% a watan Maris zuwa 1.86% a Afrilu.
"Duk da sauyin bai zo da gaggawa ba, yana nuna cewa gyare-gyaren gwamnati na yin tasiri.”

Mohammed Idris ya ce an samu sauyin ne musamman ta hanyar kulawa da farashin abinci da gwamnatin Tinubu ke yi, kamar masara, gero, wake, dawa, alkama, da shinkafa.

Gwamnatin Tinubu ta ce kudin abinci ya sauka

A bangaren kayan masarufi, Mohammed Idris ya ce an samu sauki sosai idan aka kwatanta da bara.

A cewarsa:

“Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi haifar da hauhawar farashi shi ne abinci, kuma a yanzu rahotanni na nuna ya sauka.
"Hauhawar farashin abinci ya ragu zuwa 21.26% idan aka kwatanta da bara,”

Ya ce ko da yake akwai sauran tafiya, amma hakan ya tabbatar da cewa tsauraran matakan da gwamnati ke ɗauka suna saukaka wa jama’a.

Ministan ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi talakawa, domin dawo da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki da inganta rayuwar ‘yan ƙasa.

Bola Tinubu
Gwamnatin Tinubu za ta cigaba da daukan matakan habaka tattali. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu za ta raba tallafin kudi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ya ce ta kammala tantance gidajen talakawa da za a ba tallafin kudi.

Rahotanni sun nuna cewa za a raba tallafin kudin ne ga mutane masu rauni da suke fama da matsin tattalin arziki.

Tun a baya bankin duniya ya matsa lamba wa gwamnatin Najeriya a kan ta fara raba tallafin da gaggawa ga al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng