NBS Ta Nuna yadda Farashin Kayayyaki Ya Sauka a Kasuwa a Watan Afrilu a Najeriya
- Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kaya a Najeriya ya ragu zuwa kaso 23.71 cikin 100 a watan Afrilu na 2025
- Rahoton ya nuna adadin ya ragu da kashi 0.52 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan da ya gabata, wanda hakan ke nuni da saukin hauhawar farashi
- Rahoton ya ce hauhawar farashin abinci ya ragu da 21.26% bisa alkaluman shekara-shekara, raguwar da ta kai 19.27% idan aka kwatanta da Afrilun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon rahoton da Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna saukin hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar nan.
A bisa rahoton, an samu raguwar adadin daga kashi 24.23 a watan Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu.

Asali: UGC
Daily Trust ta wallafa cewa rahoton NBS na watan Afrilu na shekarar 2025 ya nuna cewa raguwar adadin hauhawar farashi ya kai kashi 0.52 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NBS ta ce hauhawar farashin kaya na raguwa
A cewar NBS, a alkaluman wata-wata, hauhawar farashin kaya ya tsaya a kashi 1.86 a watan Afrilu, wanda ya ragu da kashi 2.04 idan aka kwatanta da kashi 3.90 da aka samu a Maris.
Wannan na nufin cewa yawan karin farashi da ake samu a kasuwanni ya ragu sosai a watan Afrilu idan aka kwatanta da watan Maris da ya gabata.
Rahoton cibiyar ya ce wannan na daga cikin alamun da ke nuni da cewa yunkurin gwamnatin Najeriya na dakile hauhawar farashin kaya yana samun nasara sosai.
Farashin abinci ya ragu da kaso mai yawa
NBS ta ce a bangaren abinci, hauhawar farashin ya tsaya a kashi 21.26 a shekarar 2025, wanda ya ragu da kashi 19.27 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a shekarar da ta gabata (40.53%).
Sai dai a wata-wata, rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashin abinci ya tsaya a kashi 2.06 a watan Afrilu, inda ya ragu da kashi 0.12 daga kashi 2.18 na Maris.
Hauhawar farashin kayan abinci na cikin manyan matsalolin da aka samu a Najeriya, musamman bayan cire tallafin man fetur.
Kayan abinci da suka rage farashi a Najeriya
Daga cikin kayayyakin abinci da suka rage farashi a Najeriya akwai fulawa, masara, alkama, doya, wake, shinkafa, da gyaɗa.
Ana sa ran cewa za a cigaba da samun saukin farashin abinci a Najeriya sakamakon wasu matakan da gwamnati ta dauka.

Asali: Facebook
BUA ya yi magana kan saukar farashin abinci
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya gana da shugaba Bola Tinubu.
Abdul Samad Rabiu ya ce farashin abinci zai cigaba da sauka sakamakon cire harajin shigo da abinci da aka yi na wata shida.
Ya kuma tabbatar da cewa ba za a kara kudi siminti ga masu yin kwangila karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba ko da farashi ya tashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng