'Yan Bindiga Sun Yi Tabargazar Sace Sarki da Dare, an Kama Mutum 5
- Rundunar ‘yan sandan Abuja ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wani hakimi, Yuda Garba, da wasu mutane biyar
- Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka aikata laifin sun kai hari kauyen Ungwan Pawa Dnako da ke kan titin Igu a Abuja
- Jami’an tsaro sun fara bincike tare da kokarin ceto wadanda aka sace, tare da shirin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Abuja ta cafke wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a sace wani hakimi, Yuda Garba da wasu mutane biyar.
Rahotanni sun nuna cewa mutane 15 dauke da makamai sun afka kauyen Ungwan Pawa Dnako a daren 11 ga watan Maris, suka yi garkuwa da mutanen kauyen.

Kara karanta wannan
Bayan hallaka jama'a da karbe kudin fansa, mugun 'dan ta'adda ya gamu da karshensa

Asali: Facebook
Zagazola Makama ne ya bayyana yadda jami'an tsaro suka kama mutane biyar a wani sako da ya wallafa a dandalin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi daga jami’an tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin ceto wadanda aka sace, tare da kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere daga yankin.
Abubuwan da 'yan sanda suka gano
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun karbi rahoton harin da misalin karfe 6:30 na safe, inda suka garzaya kauyen domin gudanar da bincike mai zurfi.
Rahotanni sun nuna cewa bayanan sirri sun bankado cewa mutanen garin sun sayar da gonakinsu kwanan nan, kuma ana zargin wasu sababbin shigowa yankin na da alaka da garkuwa.
Binciken ya nuna cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun lura da yawan shigowar mutanen da ake zargin su ne suka shirya harin.
Mutanen da aka kama bayan kai harin
Daga cikin wadanda aka kama sun hada da Abdullahi Idris, Tambaya Idris, Haruna Tukur, Umar U. Haruna da Nasiru Haruna.
Jami’an tsaro sun ce suna cigaba da bibiyar alakar wadannan mutane da garkuwa da hakimin da sauran mutanen da aka sace.
Ana kokarin ceto sarkin da aka sace
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike don ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan banga sun bazama domin bibiyar inda ‘yan bindigar suka tsere.
Bincike ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen na iya zama a wata maboya a cikin dazukan da ke kusa da yankin.

Asali: Getty Images
Jami’an tsaro sun bayyana cewa suna amfani da dabarun tsaro na zamani domin gano wuraren da ake boye mutanen da aka sace tare da kawo karshen ayyukan masu garkuwa a yankin.
Jami'an tsaro sun bukaci al’ummar yankin da su ba da hadin kai ta hanyar kawo rahotanni da za su taimaka wajen bankado maboyar masu garkuwa da mutane.
An kashe 'yan bindiga 50 a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun sojin sun ragargaji 'yan bindigar inda suka kashe 'yan ta'adda 40 a cikinsu yayin farmakin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng