Kungiya Ta Gano Manufar Masu Son a Ayyana a Ayyana Dokar Ta Baci a Zamfara

Kungiya Ta Gano Manufar Masu Son a Ayyana a Ayyana Dokar Ta Baci a Zamfara

  • Ƙungiyar PAPSD ta nuna rashin gamsuwa da kiraye-kirayen da ake yi na sanya dokar ta ɓaci a jihar Zamfara
  • Jagora a ƙungiyar, Dr. Sani Shinkafa ya bayyana cewa akwai a siyasa a cikin kiran da ake yi na ayyana dokar ta ɓaci a jihar
  • Ya bayyana cewa abubuwan da suke faruwa a Zamfara, ba su kai girman da za a sanya dokar ta ɓaci ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Kungiyar Patriots for the Advancement of Peace and Social Development (PAPSD) ta yi magana kan kiraye-kirayen da ake yi na sanya dokar ta ɓaci a jihar Zamfara.

Ƙungiyar ta bayyana kiraye-kirayen da ake yi na ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara a matsayin waɗanda aka sanya siyasa ciki, marasa tushe, rashin kishin ƙasa da kuma saɓawa kundin tsarin mulki.

Dauda Lawal
Kungiyar PAPSD ta soki kiran a sa dokar ta baci a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Daraktan gudanarwa na PAPSD, Dr. Sani Shinkafi, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene manufar masu son dokar ta ɓaci a Zamfara

Sani Shinkafi ya ce wannan kiran wani yunƙuri ne na hana zaman lafiya da tayar da hankula a jihar Zamfara.

Ya ce an shirya hakan ne domin jefa jihar cikin ruɗani da rikice-rikicen siyasa, don hana Gwamna Dauda Lawal ci gaba da irin gagarumin sauyi da yake kawo wa jihar daga dogaro da noma zuwa masana'antu.

Sani Shinkafi ya yi Allah-wadai da waɗanda ke ɗaukar matasa nauyin matasa su gudanar da zanga-zanga don a ayyana dokar ta-baci a Zamfara kamar yadda aka yi a jihar Rivers, yana mai cewa babu kamanceceniya ko kaɗan tsakanin halin da jihohin biyu ke ciki.

Ya bayyana cewa dalilan da suka sa aka ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers ba su shafi jihar Zamfara ba, musamman ma kasancewar Gwamna Dauda na mayar da hankali wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓensa.

Shinkafi ya kuma nuna cewa sashe na 188 da na 189 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa gyara sun fayyace hanyoyin da za a iya cire gwamna ko mataimakin gwamna daga muƙaminsa, yayin da sashe na 305 ke bayani kan ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta ɓaci.

Shinkafi, wanda jigo ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu-Shettima a 2023, ya ce babu wani abu da ke nuna cewa jihar Zamfara na cikin hali na yaƙi da zai buƙaci ayyana dokar ta-baci.

Ya bayyana cewa idan aka kwatanta da shekarun baya, tsaro a jihar Zamfara ya samu gagarumin ci gaba.

“Abin baƙin ciki ne yadda ake yaɗa tsofaffin hotuna da bidiyo na hare-hare a kafafen sada zumunta don tayar da zaune tsaye da ƙoƙarin ɓata sunan shugabanci mai hangen nesa na Gwamna Dauda Lawal."

- Dr. Sani Shinkafi

Shinkafi ya kuma jaddada cewa kamar yadda yake ga sauran gwamnoni, Gwamna Lawal ba shi da ikon tura jami’an tsaro kai tsaye idan an samu matsalar tsaro a wani ɓangare na jihar.

Sani Shinkafi
Sani Shinkafi ya bukaci a ba jami'an tsaro kayan aiki Hoto: Dr. Sani Shinkafi
Asali: Facebook

An ba Tinubu shawara

Ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da manyan hafsoshin tsaro su ɗauki mataki cikin gaggawa kamar yadda aka taɓa yi a baya don dakile barazanar tsaro.

A ƙarshe, ya yaba wa ƙoƙarin jami’an tsaro da suka dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kiran gwamnatin tarayya da ta kara musu kwarin gwiwa da samar da kayan aiki domin fatattakar maƙiyan asar nan.

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ramuwar gayya.a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun ƙona shaguna tare da sace dabbobi masu yawa a harin da suka kai a ƙauyen wanda yake a ƙaramar hukumar Maru.

Harin na zuwa ne bayan wasu ƴan sa-kai sun ragargaji ƴan bindiiga a wani artabu da suka yi a cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng