Magajin Rafi: Dattijon Arewa Ya Yi Murabus, Masarautar Zazzau Ta Yi Sabon Nadi
- Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara yada labarin cewa masarautar Zazzau ta tumbuke rawanin Magajin Rafin Zazzau
- Sai dai, sahihin bincike ya karyata rahotannin da ake yadawa game da nadin da masarautar ta yi, kuma an gano dalilin da ya sa aka nada Shehu Abdullahi
- Farfesa Ango Abdullahi, mai shekaru 80, tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, shi ne tsohon Magajin Rafin Zazzau da ya bar rawanin
- Amma da kansa Farfesa ya rubuta wasika ga masarauta, yana bayyana bukatarsa na a nada sabon Magajin Rafi saboda dalilan da ya bayyana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya nada Alhaji Shehu Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.

Kara karanta wannan
'Dan Sule Lamido ya bi sahun mahaifinsa, ya fadi kuskuren ƴan Najeriya a zaben 2023
Alhaji Abdullahi, mai shekaru 61, tsohon jami’i ne a ma’aikatar hukumar daidaita farashin man fetur na kasa (NMDPRA) da ke Abuja, ya rike mukamin shugabanta a bangaren kudi.

Asali: Facebook
A labarin da ya kebanta ga jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa sabon Magajin Rafin Zazzau ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Jos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da karatun digiri na biyu (MBA) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna.
Zazzau: Farfesa Ango Abdullahi ya yi murabus
Kafin nadin sabon Magajin Rafi, sarautar tana hannun Farfesa Ango Abdullahi mai shekaru 80, tsohon mataimakin shugaba a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya.
Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa Farfesa Ango Abdullahi ya ajiye mukamin ne da kansa saboda tsufa.

Asali: Facebook
Ya rubuta wa masarautar Zazzau takarda yana mai neman a nada wani wanda zai maye gurbinsa a matsayin Magajin Rafi.
Bayan wannan bukata, Sarkin Zazzau ya zabi Shehu Abdullahi, wanda shi ne ƙani ga Farfesa Ango Abdullahi, domin ci gaba da rike mukamin Magajin Rafi.
Ba a kwace mukamin Magajin Rafin Zazzau ba
A gefe guda, wasu rahotanni da suka yadu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa masarautar Zazzau ta kwace wa Farfesa Ango Abdullahi mukaminsa.
Sai dai, sahihan bayanai sun nuna cewa ya ajiye mukamin ne da kansa, kuma masarautar ba ta tilasta masa yin hakan ba.
An yabi masarautar Zazzau
A wata takarda da aka aikewa da Sarkin Zazzau, Farfesa Abdullahi ya bayyana godiyar iyalansu, a madadin marigayi Sarkin Yakawada, Alhaji Abdullahi Kwasau, bisa nadin sabon Magajin Rafi.
Haka kuma, ya tabbatar da cikakken biyayyarsu ga Masarautar Zazzau, yana mai jaddada cewa za su ci gaba da girmama da kuma mara wa masarautar baya.
Yaron Sarkin Zazzau Shehu ya rasu
A baya, mun wallafa cewa masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta sake yin rashin wani babban yarima karo na biyu a cikin wata guda, bayan da Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya riga mu gidan gaskiya.
Alhaji Ibrahim Shehu Idris, ɗan marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya rasu yana da shekaru 47 a duniya, kwanaki 21 bayan rasuwar Ɗan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris,
Marigayin shi ne mai rike da sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida na Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya kafin ya amsa kiran Mahaliccinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng