Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Ke Neman Tuge Babban Sarki daga Kujerarsa

Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Ke Neman Tuge Babban Sarki daga Kujerarsa

  • Babbar kotun a Delta ta yi watsi da karar da ke kalubalantar nadin Cif Oma Eyewuoma a matsayin Ologbotsere na masarautar Warri
  • Mai shari’a Agboje ya ce an kawo karar ba bisa ka’ida ba, inda lauyan Eyewuoma ya ce babu wata kara da ke kalubalantar nadin a yanzu
  • Masu karar ciki har da Ayiri Emami sun gaza gabatar da koke ga gwamnati kafin zuwa kotu, wanda ya sa kotu ta yi watsi da karar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Babbar kotun jihar Delta da ke Warri ta yi watsi da kara mai lamba W/112023 da ke kalubalantar nadin Cif Oma Eyewuoma a matsayin Ologbotsere.

A cikin hukuncin da aka yanke jiya Litinin, Mai shari’a V.O. Agboje ya bayyana cewa ba a kawo karar daidai ba, wanda hakan ya sa kotun ta yi watsi da ita.

Kotu ta yi hukunci a karar da ake yiwa Sarki
Kotu ta kori karar neman tuge Sarki. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wane hukunci kotun ta yi kan sarauta?

Vanguard ta ce an nada Cif Eyewuoma a matsayin Ologbotsere a shekarar 2023 bayan Olu na Warri ya cire Cif Ayiri Emami daga mukaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda rashin jin daɗi, wasu daga cikin ‘yan asalin gidan Ologbotsere da Ayiri Emami suka kai kara don a soke nadin Cif Oma Eyewuoma.

Sun nemi kotu ta bayyana cewa nadin Cif Oma Eyewuoma ya sabawa al’ada da dokar sarauta ta Bendel ta 1979, don haka ba ya da inganci.

Sun roki kotu da ta soke nadin da aka yi a watan Afrilu 2023 saboda ya sabawa al’adun Itsekiri da dokar nadin sarakuna wanda ya dawo rigimar masarauta.

Har ila yau, sun nemi kotu da ta dakatar da Cif Eyewuoma daga kiran kansa Ologbotsere na masarautar Warri har abada.

Da yake magana da ‘yan jarida bayan hukuncin, lauyan Cif Eyewuoma, Mr. Amiandamen Oriakhi, ya ce hukuncin ya nuna babu kara a gaban kotu yanzu.

Ya ce:

“Ologbotsere da Ayiri Emami sun kai karar ne suna kalubalantar nadin Eyewuoma don maye gurbin Ayiri a matsayin Ologbotsere."
Kotu ta kori karar neman tsige Sarki
Kotu ta yi fatali da korafin neman tsige Sarki. Hoto: Gov Emmanuel Ewetan Uduaghan.
Asali: Facebook

Korafe-korafe da aka shigar gaban kotu

Oriakhi ya kara da cewa sun kare kansu da hujjar cewa dukkan sarauta mallakin Sarki ce kuma yana da ikon nada wanda ya ga dama.

“Muna da wata hujja a farko cewa ba a kawo wannan kara daidai ba. Doka ta ce sai an fara kai koke ga gwamnati."

- A cewarsa

Oriakhi ya jaddada cewa masu karar ba su bi matakin kai koke ga gwamnati ba kafin su shigar da kara kotu, wanda ya sa ta zama ba ta da inganci.

Ya ce:

“Yau kotu ta yanke cewa karar Ayiri ba a kawo ta daidai ba, saboda haka ta yi watsi da ita. Babu kara yanzu a gaban kotu."

Sarki ya haramta ayyukan bokaye mata

Kun ji cewa Sarki Asagba na Asaba, Epiphany Azinge ya haramta ayyukan bokaye mata da wasu masu asiri, don dakile laifuffuka a yankin.

Hakan ya biyo bayan zargin wasu masu bokanci da hannu a kisan dan majalisa na Anambra, wanda aka gano gawarsa bayan sace masa kudi.

Wasu majiyoyi sun ce an kafa doka domin tantance mazauna Asaba tare da hana shige da ficen bata-gari a yankin domin inganta tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.