An Naɗa Gwamnan Kano Ganduje Da Matarsa Hafsat Sarauta A Jihar Delta

An Naɗa Gwamnan Kano Ganduje Da Matarsa Hafsat Sarauta A Jihar Delta

  • Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Ganduje sun samu sarauta a jihar Delta
  • Mai martaba Ohworode na masarautar Olumo, Dr Ovie Dr R.L Ogbon ne ya nada Ganduje da matarsa sarautar Olorogun na Olomu
  • Sarakuna da dama a masarautar na Olomu, iyalan Ganduje, manyan jami'an gwamnatin Kano da wasu da dama sun halarci bikin

Jihar Delta - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Umar, sun samu sarautar Olorogun na masarautar Olomu a jihar Delta a yau.

Ohworode, basaraken tsohuwar masarautar Olomu mai tarihi, mai martaba Ovie Dr R.L Ogbon ne ya nada su sarauatar, Daily Trust ta rahoto.

Nadin sarauta ta Ganduje.
An Nada Gwamnan Kano Ganduje Da Matarsa Sarauta A Jihar Delta. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Sarakuna, manyan jami'an gwamnatin Kaduna da iyalan Ganduje sun halarci nadin

Bikin da aka yi a fadar Ohworode na masarautar Olomu ta samu halartar mutane da dama da suka hada da sarakuna daga masarautar Olomu, manya a gwamnatin jihar Kano, iyalan gidan Ganduje, yan siyasa da sauran yan masarautar Olomu, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Kungiyar Matan Zamfara Sun Ayyana Wanda Zasu Zaba Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotuna: Tinubu Da Wasu Manya a Najeriya Sun Halarci Nadin Sarautar Ganduje Da Gwaggo a Ibadan

A baya, mun rahoto cewa a Asabar 18 ga watan Yuni ne aka nada gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Farfesa Haftsat Ganduje sarauta a masarautar Ibadan.

Mai martaba Olubadan na Ibadan, Dakta Lekan Balogun ya nada Ganduje sarautar Aare Fiwajoye ita kuma Hafsat aka nada ta sarautar Aare Fiwajoye, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Wasu manyan mutane a Najeriya sun samu halartar nadin sarautar cikinsu har da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2022 kuma jagoran jam'iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel