An Yi Babban Rashi a Kano, Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Rasu Yana da Shekaru 63
- Abdulkadir Yusuf Guɗe, tsohon ɗan takarar gwamnan Kano da tsohon Sakataren Ƙungiyar NRO, ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 63
- Daya daga cikin aminansa, Malam Hamisu Umar Yakasai ya bayyana Guɗe a matsayin jagora mai sadaukar da kai, ɗan kishin ƙasa, kuma mai son kawo sauyi
- Guɗe na daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP a jihar Kano, kuma an san shi da hidimar jama'a a matakin siyasa da zamantakewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Abdulkadir Yusuf Guɗe, tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Kano, ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
Kafin rasuwarsa, Guɗe shi ne tsohon Sakataren Kungiyar Northern Reform Organisation (NRO), masu fafutukar kawo ci gaba a Arewacin Najeriya.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, ɗaya daga cikin abokansa na kut-da-kut da kuma ɗan ƙungiyar NRO, Malam Hamisu Umar Yakasai, ya tabbatar da rasuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ɗan takarar gwamna ya rasu a Kano
Abubakar Dangambo ya wallafa a shafin Facebook cewa daya daga cikin makusantan marigayin Mahmoud Adnan Audi ya tabbatar da rasuwar Alhaji Abdulkadir.
Rahotannin sun tabbatar da cewa Abdulkadir Yusuf Guɗe ya rasu da safiyar ranar Juma’a bayan doguwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Ya ce:
“Mun rasa wani muhimmin mamba na al’umma, jagora mai sadaukarwa, kuma aboki na gaske ga mutane da dama,."
Kokarinsa na samar da ci gaba, ƙwarewarsa da jajircewarsa sun bar tarihi a zukatun duk wanda ya san shi."
Kano: An yi alhini kan rasuwar Gude
An san marigayi Abdulkadir Yusuf Guɗe, wanda shi ne ɗaya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a jihar Kano, saboda tasirin da ya yi a siyasar jihar.
Ana kuma yi masa kallon gwarzo, wanda ya sadaukar da kansa wajen hidimar al’umma, kuma ana ganin shi ɗan siyasa mai kishin samar da sauyi.

Asali: Facebook
A sanarwar da kungiyar NRO ta fitar, ta bayyana mamacin da cewa ba yana son duk cigaban jama'a da gudanar da siyasa domin inganta rayuwar jama'a.
Sanarwar ta kara da bayyana shi da cewa:
“Mutum ne mai halin kirki, jagoran al’umma, mai sanin ya kamata, kuma ɗan kishin kasa.”
Kungiyar ta ƙara da cewa rashin sa zai bar babban gibi a zukatan abokan aiki, abokai, da duka waɗanda suka yi aiki tare da shi.
Fitaccen dan siyasa ya rasu a Kano
A baya, mun wallafa cewa an tabbatar da rasuwar fitaccen ɗan siyasa kuma shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Ambasada Ahmadu Haruna Zago, wanda aka fi sani da Ɗanzago.
Ya rasu bayan ya sha fama da rashi lafiya, wanda gabanin komawarsa da Mahalicci, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya nada Zago a matsayin shugaban REMASAB a ranar 5 ga watan Yuli, 2023.
Ɗanzago ya shahara a siyasance a matsayin jigo a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa, inda ya rike shugabancin wani tsagi na jam’iyyar lokacin da rikici ya dabaibaye shugabancin APC a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng