"Mulkinka Ya Zo da Alheri," Sarakuna Sun ba Shugaba Tinubu Sabuwar Sarauta

"Mulkinka Ya Zo da Alheri," Sarakuna Sun ba Shugaba Tinubu Sabuwar Sarauta

  • Sarakunan gargajiya a jihar Anambra sun karrama shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sarautar, 'Dike si mba Anambra' watau baƙon jarumi
  • Shugaban majalisar sarakunan jihar, Eze Chidubem Iweka ya ce sun ba Tinubu sarautar ne saboda kyawawan ayyukan da yake yi a faɗin Najeriya
  • Bola Tinubu ya gode wa sarakunan bisa karramawar da suka masa, inda ya bukaci ƴan Najeriya su haɗa kai don ci gaban ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Sarakunan gargajiya na Jihar Anambra sun karrama Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sarautar “Dike si mba Anambra” wato “Baƙon Jarumi.”

Sarakunan da suka fito daga sassa daban-daban na jihar Anambra sun ba Tinubu wannan sarauta ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya.

Bola Tinubu da sarakuna.
Sarakunan Anambra karrama Shugaba Tinubu da sarautar gargajiya Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kai ziyara ne domin kaddamar da muhimman ayyuka da Gwamna Chukwuma Charles Soludo ya kammala a filin Alex Ekwueme da ke Awka, babban birnin Anambra.

Me yasa sarakuna suka ba Tinubu sarauta?

Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, Eze Chidubem Iweka, ya ce an ba Tinubu sarauta ne a madadin sarakunan gargajiya daga dukkanin yankuna 179 da ke fadin Anambra.

Basaraken ya ce sun yanke shawarar naɗa shugaban ƙasa sarautar saboda yabawa da irin kokarin da ya ke yi a fadin Najeriya tun da ya karɓi mulki.

“Wannan sarauta ce daga dukan sarakunan gargajiya na Jihar Anambra. An ba ka ne da sunan ‘Dike si mba Anambra’, wanda ke nufin ‘baƙon jarumi’, domin karramawa bisa kyawawan ayyukan da kake yi a ƙasar nan.
"Mun ga ci gaba a fannin ababen more rayuwa da suka hada da manyan hanyoyi, musamman hanyoyin da suka hade da Gadar Kogi ta biyu, da kuma wasu ayyuka a garuruwanmu.

"Allah ya kara ba ka hikima wajen tafiyar da shugabanci yadda ya dace a Najeriya.

- In ji Eze Chidubem Iweka.

Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya kwashi gaisuwa, ya godewa sarakunan Anambra Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya godewa sarakuna

Shugaban kasa Tinubu ya bayyana jin dadinsa da godiya kan wannan sarauta, yana mai cewa Najeriya za ta ci gaba ne idan jama'a suka haɗa kansu

“Wannan girmamawa da kuka yi mani za ta shiga tarihi a rayuwata. Dole ne mu hada kai a matsayinmu na ‘yan kasa domin mu gina Najeriya,” in ji Tinubu.

Cikin manyan baki da suka halarci taron akwai: Mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu; gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun da na Imo, Hope Uzodimma.

Sauran sun kunshi gwamnan Abia, Alex Otti; na Enugu, Peter Mbah; da kuma Ministan Ayyuka, Dave Umahi.

Bola Tinubu ya yabi Gwamna Soludo

A wani labarin, kun ji cewa mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamna Charles Soludo bisa ayyukan ci gaban da yake yi a jihar Anambra.

Bola Tinubu ya isa Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ranar Alhamis a wata ziyarar kwana ɗaya domin ƙaddamar da muhimman ayyukan Soludo.

Shugaban ya bayyana gamsuwarsa da nasarorin da gwamnan ya cimmawa a zangon mulkinsa na farko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262