Ahmad Lawan: Tsohon Shugaban Majalisa Ya Fayyace Gaskiyar Shirin Barin APC zuwa SDP
- Tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rahotannin da ke cewa yana shirin barin APC zuwa jam'iyyar SDP
- Sanata Ahmad Lawan ya musanta cewa yana shirin barin jam'iyyar wacce ya kasance a cikinta tun bayan kafuwarta
- Ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a jam'iyyar, inda ya bayyana rahotannin shirin komawa SDP a matsayin ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya yi magana kan batun shirin ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP.
Sanata Ahmad Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin APC domin komawa jam’iyyar SDP.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmad Lawan ya musanta shirin barin APC
Sanata Ahmad Lawan ya jaddada cewa bai da shirin ficewa daga jam’iyyar mai mulki, yana mai cewa yana nan daram a cikinta.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ƙara da cewa yana nan a matsayin mamba mai biyayya da cikakken goyon baya ga APC, jam’iyyar da ya kasance cikinta tun kafuwarta, kuma ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gabanta.
Ya ce zai ci gaba da kasancewa jigo a jam’iyyar APC, tare da aiki kafada da kafada da jam’iyyar da gwamnatin tarayya domin cimma manufofin su na bai ɗaya.
Tsohon shugaban majalisa bai shirin komawa SDP
“Ofishin Sanata Ahmad Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa ta tara kuma mai wakiltar Yobe ta Arewa, ya samu rahotannin da ba su da tushe ko makama masu cewa yana shirin barin jam’iyyar APC domin komawa SDP."
"Muna so mu bayyana a fili cewa waɗannan rahotannin ƙarya ne, babu gaskiya a cikinsu, kuma babu wata hujja da ke tabbatar da su."

Kara karanta wannan
Kwanaki da sauya shekar El-Rufa’i, ana ganin alamun rigimar takarar Shugaban kasa
"Sanata Ahmad Lawan yana nan daram a jam’iyyar APC, jam’iyyar da ya kasance cikinta tun kafuwarta, kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa a cikinta."
"Har yanzu yana ɗaya daga cikin manyan ƴan jam’iyyar APC kuma zai ci gaba da aiki tare da ita da kuma gwamnati domin tabbatar da nasarar manufofin su na bai ɗaya."
"Yana da kyau a sani cewa, a tsawon shekarun siyasarsa da suka kai shekara 25 a majalisa, Sanata Ahmad Lawan yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar Najeriya da ba su taɓa sauya sheka ba tun farkon shigarsu siyasa."
"A shekarar 1999 ne aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai, sannan daga bisani ya koma majalisar dattawa a shekarar 2007, ƙarƙashin jam’iyyar APP, wacce daga baya aka sake mata suna zuwa ANPP."
"Jam’iyyar ANPP na ɗaya daga cikin jam’iyyu uku da suka haɗu suka kafa jam’iyyar APC a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2013."
- Ezrel Tabiowo
Sanata Ahmad Lawan ya koka kan yunwa a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya koka kan halin yunwa da ƴan Najeriga suka tsinci kansu a ciki.
Sanatan Ahmad Lawan ya yi kira ga shugabanni da su yi gaggawar ɗaukar matakin domin magance matsalar halin yunwar da ke fama da shi.
Asali: Legit.ng