Tsaro: Akpabio Ya Gargadi Badaru, Ya Ce kar Ya Hada Majalisa Fada da Tinubu

Tsaro: Akpabio Ya Gargadi Badaru, Ya Ce kar Ya Hada Majalisa Fada da Tinubu

  • Majalisar dattawa ta gargadi ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar kan kalamansa da ka iya janyo sabani da fadar shugaban kasa
  • Godswill Akpabio ya bayyana cewa kin amincewa da taron tsaro da majalisar ke shiryawa ba zai taimaka wajen kawo zaman lafiya ba
  • Majalisar dattawa ta ce kamata ya yi jami'an gwamnati su rika warware sabani ta hanyar tuntubar juna ba jefa kalamai a bainar jama’a ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta nuna rashin jin dadin kan kalaman ministan tsaro, Mohammed Badaru, da ta ce na iya haddasa sabani tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa.

Hakan ya biyo bayan furucin da Badaru ya yi cewa ba a bukatar shirin taron tsaro da majalisar dattawa ke shiryawa na kwana biyu domin warware matsalolin kasar.

Badaru
Majalisa ta gargadi Badaru kan raddin da ya mata game da tsaro. Hoto: Nigerian Senate|Mati Ali
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Opeyemi Bamidele, sun bayyana haka ne a zaman majalisa da aka gudanar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ce irin wannan furuci na iya tauye kokarin da majalisa ke yi wajen tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a fannin na tsaro.

A cewar su, yana da kyau ministoci su rika tuntubar shugabannin majalisa kafin su bayyana ra’ayoyinsu kan kudurorin da suka shafi harkokin kasa.

Me ministan tsaro ya fada?

A yayin wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, Badaru ya ce rundunar sojin Najeriya yanzu na da kayan aiki da dabaru fiye da 'yan ta’adda.

Badaru Abubakar ya ce za a fi inganta tsaro ida aka dogara da samar da dabaru masu karfi fiye da shirya taruka.

Ministan ya ce:

“Dabarun aiki su ne abin da ke kawo nasara, ba taruka ba.

"Za a iya samun shawarwari yayin taro, amma umarnin aiki daga manyan hafsoshin tsaro ya ke zuwa, ba daga tattaunawa a bainar jama’a ba,”

Kalaman sun jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin sanatoci da dama, inda suka bayyana su a matsayin barazana ga kokarin da majalisar ke yi wajen hada kai da gwamnatin tarayya.

Akpabio ya gargadi Badaru kan taron tsaro

Da yake mayar da martani, Akpabio ya ce bai dace da minista ya bayyana rashin goyon bayansa ga kudurin majalisa a bainar jama’a ba.

Badaru
Akpabio ya nuna rashin jin dadi kan kalaman Badaru. Hoto:; Mati Ali
Asali: Facebook

Shugaban majalisar ya ce idan akwai wani sabani, kamata ya yi a tunkari shugabancin majalisa kai tsaye.

Akpabio ya ce:

“Ina kira ga ma’aikatar tsaro da kada ta rika warware matsaloli a kasuwa.
"Ya kamata su tuntubi shugaban majalisa ko dattawan majalisa. Kalamai a bainar jama’a ba za su taimaka ba, sai dai su kara dagula lamarin tsaro,”

Akpabio ya maka Sanata Natasha a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya kara shigar da karar Sanata Natasha Akpoti a gaban kotu.

Godswill Akpabio ya kai Natasha kotu ne bisa wasu kalamai da ta yi cikin barkwanci game da ba shi hakuri.

Shugaban majalisar dattawan ya bukaci Sanata Natasha ta ba shi hakuri a jaridu biyu na kasa a kan sakon da ta wallafa a Facebook.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng