A kalla yara 5 na ja cikin kungiyar asiri - Matashi mai shekaru 20

A kalla yara 5 na ja cikin kungiyar asiri - Matashi mai shekaru 20

Wani wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne mai shekaru 20 mai suna Somtochukwu Onyebuchi, ya bayyana cewa ya ja kananan yara biyar zuwa kungiyar asirin a jihar Anambra.

Wanda ake zargin, mai aski ne a kauyen Ire da ke Ogidi, karamar hukumar Idemili ta jihar. Yana daga cikin wandanda ake zargi 103 da rundunar 'yan sandan ta damke.

Ya dora laifin a kan shaidan tare da jan kunnen wadanda har yanzu ke cikin kungiyar da su fice, The Nation ta ruwaito.

Ya ce: "Na kasance dan kungiyar asiri ta JVC tun a 2015 kuma na ja kananan yara biyar ciki. Na san hanyar jan hankalin kananan yaran.

"Na yi nadamar shiga wannan harkar saboda ba zan ce ga abinda na karu da shi ba tun bayan shigata kungiyar. Ina shawartar sauran 'yan kungiyar da su tuba kafin a kama su."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya ce wanda ake zargin ya kware wurin jan ra'ayin kananan yara zuwa kungiyar asiri kuma 'yan sandan suna nemansa tuni.

Ya ce: "Wanda ake zargin an kama shi wurin karfe 5 na asuba bayan samamen da jami'an tsaro suka kai.

"Ya ja kananan yara da yawa kungiyar kuma kananan yara biyu ne suka kai jami'an maboyarsa."

Ya ce za su gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

A kalla yara 5 na ja cikin kungiyar asiri - Matashi mai shekaru 20
A kalla yara 5 na ja cikin kungiyar asiri - Matashi mai shekaru 20. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Buratai ya zoyarci sojin Najeriya da ke jinya a Kaduna (Hotuna)

A wani labari na daban, 'yan sanda sun damke wasu matasa 25, mata 10 da maza 15, a yayin da ake zargin su da yin bidiyon batsa a yankin Kakamega da ke kasar Kenya. Matasan da suka raba kansu biyu-biyu da uku-uku na da shekaru 13 zuwa 17.

Shugaban wadanda ake zargin kuma mashiryin fim din sunansa Caleb. Wani ganau ba jiyau ba mai sana'ar kwashe bola, ya ce hankalinsa ya kai kansu ne yayin da ya tsinta Leda baka cike da kwaroron roba.

Ya ga matasan na lalata yayin da wani ke nada a bidiyo. Tuni ya kira jami'an 'yan sanda.

Ganau ba jiyau ba ya ce; "Ina aikina na kwashe shara ne na ga wani abun mamaki. Na samu kwaroron roba masu yawa a bakar leda sannan na ji hayaniya daga wani gida.

"A lokacin da na shiga gidan, na sha matukar mamaki domin kuwa mata na ga suna lalata kuma wani mutum yana nada.

"A take na sanar da 'yan sanda kuma da gaggawa suka iso inda suka kama wadanda ake zargin. Sun yi lalata da kwaroron roba yayin da wasu suka yi babu shi."

OCPD na yankin Kakamega, David Kabena ya tabbatar da kamen. "Duk wadannan kananan yara da muka kama suna lalata za mu ladabtar da su. Za mu tsananta horo ga Caleb don shine yake batar da su," cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel