Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

- Dalibar makarantar sakandare GSS Ikot Ewa, jihar Cross Rivers da aka da bindiga a makaranta ta ce bindigar na saurayinta ne magidanci da yara shida

- Dalibar ta kuma bayyana cewa tana cikn wani kungiyar yan asiri mai suna 'Sky Queens' amma dai bata da wani mukami a kungiyar

- Saurayin a bangarensa ya ce bindigar nasa ne amma ba shi ya bata ba, ita da kanta da dauka a karkashin gadonsa inda ya ke ajiye wa

- Rundunar yan sandan jihar Cross Rivers bayan kama saurayin da yarinyar ta ce za ta zurfafa bincike a kan lamarin

Matashiyar dalibar da aka kama da bindiga a makaranta ta amsa cewa tana cikin kungiyar yan asiri. Ta kuma ce a wurin saurayinta, Okon Effingham, wanda ke da aure da yara shida ta karbo bindigar, rahoton jaridar Vanguard.

Da farko an yi ikirarin cewa dalibar, yar makarantar sakandare ta gwamnati na Ikot Ewa, jihar Rivers ta tafi da bindigar makaranta ne domin harbin malaminta da ya ce ta aske gashinta da ta rina.

Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta
Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

Amma bayan kama ta, yan sanda sun gano cewa za ta kai bindigan wurin wani makeri ne.

Ta shaidawa manema labarai a ranar Juma'a 19 ga watan Fabrairu yayin da ake holen ta tare da saurayinta wanda suka fara soyayya tun Agustan 2020 cewa shine ya mallaki bindigar.

Ta kara da cewa mutumin yana taimaka mata da wasu abubuwa amma ba shi ke biyan kudin makarantar ta ba.

KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

Ta ce mahaifiyarta na barin mutumin ya kwana a dakinta inda ya zo gidansu ziyara.

Da ta ke magana a hedkwatar yan sanda, Diamond Hill, Calabar, yayin holen ta da saurayinta wanda ya mallaki bindigar wasu 11 domin aikata laifuka, ta ce, "Ni yar kungiyar asiri na Sky Queen ne, bani da mukami a kungiyar, na san wanda ya mallaki bindigar tun bara, ya kan zo gidan mu ya kwana kuma ya kan taimaka min da kananan abubuwa, amma ba shi ke biya min kudin makaranta ba."

A bangarensa, saurayin yar makarantar, Okon Effiong ya ce, "Ina da aure da yara shida, ban bata bindigar ba, dauka ta yi da kanta daga karkashin gado inda na ajiye."

Ya kuma ce suna soyayya kuma mahaifiyarta ta sani domin yana da nufin aurenta.

Kwamishinan yan sandan jihar Cross River, Sikiru Akanda ya ce za a cigba da zurfafa bincike sannan ya yi kira ga iyaye su rika kusantan yaransu don sanin wadanda suke harka da su.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164