JAMB: Mahaifin da Ya Rubutawa Yaronsa Jarabawar UTME 2024 Ya Shiga Hannun Hukuma

JAMB: Mahaifin da Ya Rubutawa Yaronsa Jarabawar UTME 2024 Ya Shiga Hannun Hukuma

  • Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta kama wani uba da laifin rubutawa dansa jarabawar UTME ta 2024
  • Farfesa Ishaq Oloyede, shugaban JAMB ya ce hukumar ta na da kayan aikin da za ta binciko masu sojan gona da satar amsa
  • Oloyede ya jaddada cewa hukumar JAMB ta dakile duk wata hanya ta magudin jarabawa yayin da yake nuna damuwa kan halayen wasu iyaye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - An kama wani uba da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba saboda rubutawa yaronsa jarabawar shiga manyan makarantu (UTME) ta shekarar 2024.

UTME 2024: JAMB ta dauki mataki kan uba da ya rubutawa dansa jarabawa
Oloyede ya ce JAMB ta kama mahaifin da ya rubutawa yaronsa jarabawar UTME. Hoto: JambOfficial
Asali: Facebook

JAMB ta damu kan magudin jarabawa

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba cibiyoyin zana jarabawar UTME a jihar Kaduna a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oloyede ya nuna fushinsa kan masu satar amsar jarabawa da kuma masu yin sojan gona yayin da yake nuna muhimmancin kama mahaifin yaron domin zama misali ga 'yan baya.

A cewar jaridar The Nation, Oloyede ya koka da irin tarbiyyar da iyaye ke nunawa yaran da ke tasowa a wannan zamani.

Mahaifi ya rubutawa dansa JAMB

Shugaban hukumar JAMB ya ce an samu nasarar cafke mutumin ne saboda hukumar ta dauki matakan da suka sha gaban tunanin masu sojan gona.

"Mun damke uba yana rubuta wa dansa jarabawa, akwai damuwa ga irin tarbiyyar da ake ba yara a zamanin nan, ina mamakin me uban zai gaya wa dan idan aka kulle su a daki daya.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: An gargadi Tinubu ya dauki mataki kan EFCC game da tsohon gwamna

"Yanzu hukumar JAMB na da dukkanin kayan aiki na kama wadanda ke satar amsar jarabawa da masu yin sojan gona domin zanawa wasu."

Oloyede, ya kuma godewa iyaye bisa goyon bayansu da kuma bin dokoki da ka'idojojin hukumar JAMB, jaridar The Guardian ta ruwaito.

An rufe makarantar Lead British

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa mahukunta sun rufe makarantar kudi ta Lead British da ke Abuja biyo bayan zargin an ci zarafin wata daliba a makarantar.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade soshiyal midiya an ga yadda wata daliba ke shararawa wata daliba mari tari da hantararta kan wani dalili da ba a gano ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel