Babu ranar daina satar jarabawa a Arewa sai an yi abubuwa biyu, Farfesa Salisu Shehu

Babu ranar daina satar jarabawa a Arewa sai an yi abubuwa biyu, Farfesa Salisu Shehu

  • Shugaban jami'ar Al-Istiqama dake jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace babu ranar daina satar jarabawa a arewa har sai an ɗauki matakai
  • Babban malamin addinin yace al'ummar Arewa sun lalace ta yadda basu damu da wace hanya aka bi ƴaƴansu suka samu sakamakon jarabawa ba
  • A cewarsa ɗaya daga cikin abinda ke kara yawaitar maguɗin shine fifita kwali fiye da kwarewar da mutum yake da ita

Kano - Shugaban jami'ar Al-Istiqama dake Sumaila jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace babu ranar daina magudin jarabawa a arewa har sai an ɗauki matakai biyu.

A wata fira da ya yi da wakilin mu na Legit.ng Hausa, Farfesan yace ainihin abinda ke kara rura wutar satar jarabawa a Arewa shine rashin tsoron Allah da lalacewar al'umma.

Bugu da ƙari, shugaban jami'ar, kuma kwararre a ilimin shari'a yace al'ummar Arewa ta gurbata ta yadda kowa ya amince da rayuwar ƙarya da ha'inci.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Farfesa Salisu Shehu
Babu ranar daina satar jarabawa a Arewa sai an yi abubuwa biyu, Farfesa Salisu Shehu Hoto: Salisu Shehu
Asali: Facebook

Ina matsalar take?

Malamin yace abin takaicin shine tun daga shugabanni, iyaye, malamai da yaran kansu, sun yarda da rayuwar ƙarya, rashin gaskiya da ha'inci, wanda a mahangarsa sune musabbabin yawaitar maguɗin jarabawa .

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abu na biyu, farfesan yace wannan yadda da karya, ha'inci da rashin gaskiya ya jawo rugujewar ilimi baki ɗaya a yankin.

A jawabinsa yace:

"Ilimi ya rushe a Arewa, saboda haka ba abinda ya yi saura banda ƙarya a cikin harkar ilimin, don haka dole ba yadda za'a yi, satar jarabawa za'a cigaba da yi kuma ba ranar daina wa."

Ina mafita?

Babban malamin addinin ya bayyana cewa matukar dagaske ana son fita daga wannan ƙangin to dole al'ummar Arewa su yi abu biyu.

A cewarsa ya zama wajibi yan arewa sun canza tunaninsu, su koma rayuwa ta gaskiya kuma su rungumi tafarkin gaskiya.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

Malamin yace:

"Duk wani gyara da aka ɗauri ɗamarar za'a yi, muddin akwai iyaye da basu damu da ƴaƴansu su zo da sakamakon ƙarya ba."
"Muddin akwai shugabanni da hukumomin ilimi da ba su damu makarantu su samu sakamako mai kyau, alhali ƙarya ne, kuma ba abinda ya jawo haka sai yarda da rayuwa ta ha'inci, to babu ranar daina satar jarabawa."

Ta ya za'a kawo ƙarshen maguɗin jarabawa a arewa?

Da aka tambayesa kan hanyoyin da za'a bi domin kawo ƙarshen lamarin, malamin yace wannan babban aiki ne mai girna.

A cewarsa ba ƙaramin dagewa za'a yi ba a kawar da maguɗin jarabawa a Arewa domin waɗanda suka ci gajiyar satar jarabawar suke koyar da ilimin.

"Sai an yi ta maza sannan za'a iya tunɓuke satar jarabawa a arewa domin akasarin malaman dake koyarwa a makarantu har jami'a sun ci gajiyar maguɗin."
"A halin yanzun, malaman Firamare, Sakandire da jami'o'i sun ci gajiyar maguɗin jarabawa, ta ya ba za'a yi satar jarabawa a ƙarƙashinsu ba?"

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun hallaka yayin da miyagun yan Bindiga suka farmaki barikin Sojoji a Sokoto

Wata babbar matsala

Daga ƙarshe shugaban jami'ar Al-Istiqama yace daga cikin abubuwan dake kara yawaitar satar jarabawa shine fifita satifiket a kan kwarewar mutum wajen ɗaukar aiki.

Idan ɗalibi ya gama karatu, sam ba'a damu da kwarewar da ya yi ba, sai kwalin karatun da ya zo da shi, inji shi.

Bisa wannan dalili ne yasa ɗalibai ke tsere da faɗawa cikin halaka domin kawai su samu kwali mai kyau, don shine zai sa su samu aiki mai gwaɓi.

"Kwarewa a banza take matukar kwalinka ba mai kyau bane, don haka wannan na daga cikin abinda ke ƙara yawan maguɗin jarabawa."

A wani labarin kuma Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta samu koma baya a jihar Gombe, yayin da jiga-jiganta aƙalla 15 suka koma jam'iyyar PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan Gombe, Lazarus Yoriyo, yace sun ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda abinda ke faruwa a ciki.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel