Amarya ta rasu a gobara kwanaki uku da tarewarta a gidan Mijinta (Hotuna)

Amarya ta rasu a gobara kwanaki uku da tarewarta a gidan Mijinta (Hotuna)

- Gobara ta yi ajalin wata Amarya kwanaki uku da bikinta

- Gobarar ta yi sanadiyyar konewar komai a gidan kurmus

Duniya budurwar wawa inji bahaushe, haka zalika masu iya magana na cewa mutuwa guda ce, amma sanadinta dayawa, kwatankwacin haka ne ya faru ga wata sabuwar Amarya da ta rasu kwanaki uku da aurenta.

Wata kawar wannan Amarya mai suna Safiyya Idris ce ta bayyana wannan labara mai tayar da hankali a ranar 18 ga watan Maris a shafinta na kafar sadarwar zamani, Facebook,kamar yadda Legit.ng ta gano.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba zan bayyana niyyar tsayawa takara ko akasin haka ba- Buhari

A cewar Safiyya, Amaryar mai suna Nana ta gamu da ajalinta ne a sakamakon wata gobara da ta taso a gidanta, kwanaki uku kacal da tarewarta da Angonta Jabeer, sai dai ba’a bayyana garin da wannan lamari ya auku ba.

Majiyar ta ruwaito cewar a ranar 0/03/2018 aka daura auren Nana, inda suka yi gobara a ranar 13/03/2018, tsananin gobarar ta kai ga cewa komai a gidan yak one kurmus, amma rahotanni sun nuna cewa mijin nata bai mutu ba.

Amarya ta rasu a gobara kwanaki uku da tarewarta a gidan Mijinta (Hotuna)
Amarya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: