Akpabio Ya Yi Kakkausan Martani ga Masu Neman Ya Yi Murabus saboda Natasha

Akpabio Ya Yi Kakkausan Martani ga Masu Neman Ya Yi Murabus saboda Natasha

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce matsin lamba daga kungiyoyin fararen hula ba zai tilasta masa murabus ba
  • Akpabio na fuskantar matsin lamba saboda takaddama a tsakaninsa da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan wacce ta yi zargin ya ci zarafinta
  • Baya ga haka, akwai batun hukuncin kotu a kan Farfesa Peter Ogban da ya murde zaben 2019 domin amfani da sakamakon don amfanar Akpabio

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga mukaminsa ba duk da matsin lamba da yake fuskanta daga kungiyoyin fararen hula.

Ana zargin Akpabio da cin zarafin daya daga cikin matan da ke majalisada kuma hannu a murde zaben 2019 a Anambra, abin da ya jawo suka daga sassa daban-daban na al'umma.

Akpabio
Sanata Akpabio ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa an dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya, bayan takaddama da Akpabio dangane da yadda aka tsara zaman kujeru a majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ana ta kai ruwa rana a kan batun ne, Sanata Natasha ta fito da zargin cewa ya dade yana neman ya ci zarafinta a baya.

Godswill Akpabio ya yi magana kan yin murabus

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin zaman majalisar ranar Alhamis, Akpabio ya maida martani ga kalaman shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele.

Akpabio ya ce zarge-zargen da ake yi masa ba su da tushe balle makama, kuma ba zai bar kansa ya fada tarkon rashin adalcin da aka dana masa ba.

Akpabio
Sanata Akpbaio ya dage a kan ce sharri ake masa kan batun Natasha Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Ya ce:

“Da ba zan amsa ba, sai dai saboda ka ambaci cewa wasu sun ce in yi murabus. Waye ya fada maka cewa zan sauka daga kujerar nan?”

“Idan ka kalli tarihi a Amurka, akwai bakaken fata da aka daure bisa rashin adalci da zargin karya. Wasu sun shafe shekaru 25 a kurkuku.”
“Ba na daga cikin irin wadannan mutane da zan sauka daga mukamina saboda zargin karya.”

Akpabio na fuskantar matsin lamba

Baya ga takaddama da Sanata Natasha, hukuncin da kotu ta yanke kan Farfesa Peter Ogban, wanda aka samu da laifin murde zabe a 2019 domin amfanar Akpabio, ya kara jawo masa matsala.

Daily Post ta ruwaito cewa kungiyoyi da dama ciki har da CISLAC, SERAP, CITAD, BudgIT da Amnesty International Nigeria sun bukaci Akpabio ya sauka daga kujerarsa.

Sai dai a martaninsa, Sanata Akpabio ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba saboda zargin karya, kuma ya bukaci sanatoci su mayar da hankali kan harkokin da za su inganta hadin kai da ci gaban kasa.

Sanata Akpabio ya caccaki Obi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya maida martani mai zafi ga tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, bisa kalamansa .

Akpabio ya yi wannan martani ne a ranar Alhamis, yayin bikin bankwana da gawar marigayi Cif Edwin Clark, tsohon ministan yaɗa labarai kuma jigo a siyasar Kudu maso Kudu.

Ya ce Obi bai kamata ya rika sukar shugabannin da suka gabata ba, alhali bai iya shawo kan matsalolin da ke addabar ƙaramar jam’iyyarsa yayin da zabe ke gabatowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.