Masu Amfani da Manhajar ‘Facebook’ Na Kasuwanci Za Su Fara Biyan N27k A Wata Kan Tantancewa

Masu Amfani da Manhajar ‘Facebook’ Na Kasuwanci Za Su Fara Biyan N27k A Wata Kan Tantancewa

  • Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya sanar da adadin kudaden da wadanda aka tantance za su fara biya
  • Mark na magana ne ga masu amfani da manhajojin ‘Facebook’ da ‘Instagram’ masu alamar tantancewa
  • Wannan na zuwa bayan mai kamfanin Twitter, Elon Musk ya sanar da cewa za su fara karbar kudade ga masu amfani da X

Kamfanin Meta wanda ya hada da ‘Facebook’ da ‘Instagram’ zai fara karbar kudade a wata ga masu amfani da su.

Kamfanin ya ce kudaden da za a biya na tantancewa ne da wasu sabbin tsare-tsare.

Masu amfani da 'Facebook' za su fara biyan kudi duk wata
'Facebook' zai kawo sabon tsarin biyan kudi duk wata. Hoto: Bloomberg/Contributor.
Asali: Getty Images

Me ye kamfanin 'Facebook' ya ce?

Legit ta tattaro cewa shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg shi ya bayyana haka yayin wani taro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Tankaɗe da Rairaya, Ya Kori Wasu Manyan Ma'aikata

A farkon wannan shekara kamfanin ya kaddamar da alamar tantancewa mai launin shudi da za a na biyan kudi Naira dubu 27 duk wata.

Kamfanin ya ce hakan zai ba da damar tallace-tallace da kuma kariya ga mai amfani da su.

A takaice idan mutum ya na son tantancewar ‘Facebook’ ko ‘Instagram zai biya Dala 22 ko duka biyun a kan Dala 35, cewar The Verge.

Wane tsari kamfanin 'Facebook' ya ke shirin yi?

Farashin zai iya karuwa a wani lokaci ga mai amfani da manhajojin daga Dala 12 zuwa 15.

Kamfanin zai fara da ‘Facebook’ da ‘Instagram’ a makwanni ma su zuwa kafin daga bisani ya juyo kan manhajar ‘WhatsApp’.

Kamfanin ya yi alkawari ga masu manhajar ta bangaren kasuwanci irin garabasar da za a bai wa ma su amfani da manhajojin na karan kansu.

Mutane da dama na korafin irin wadannan tsare-tsare tun bayan da kamfanin X ya sanar da fara karbar kudaden.

Kara karanta wannan

Elon Musk Ya Bayyana Shirin Fara Biyan Kudi Duk Wata Ga Masu Amfani Da Twitter, Ya Bayyana Dalili

Masu amfani da Twitter za su fara biyan kudi a wata, Elon Musk

A wani labarin, shugaban kamfanin Twitter, Elon Musk ya bayyana cewa masu amfani da manhajar X da aka fi sani da Twitter za su fara biyan kudi dan kadan a duk wata.

Musk ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da Fira Ministan Isra’ra, Benjamin Netanyahu.

Ya bayyana cewa kudaden ba wasu ma su yawa ba ne da kamfanin zai na karba duk wata a wurin kwastomominsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel