Rikicin Tibi da Jukun: An babbake gidaje 300 a Taraba

Rikicin Tibi da Jukun: An babbake gidaje 300 a Taraba

Akalla gidaje 300 aka babbake a ranar Asabar yayin sabunta rikici a tsakanin kabilar Jukun da Tibi a jihar Taraba.

Ana zargin tsagerun kabilar Jukun ke da alhakin kai wannan mummunan hari na ranar Asabar cikin wani kauye na 'yan kabilar Tibi, Tor-Damsa, da ke karkashin karamar hukumar Donga a jihar Taraba.

Wannan mummunan hari ya jefa dubunnan mutane cikin halin ni 'ya su a sanadiyar salwantar muhallansu kamar yadda wani mai ba da shaida ya labartawa manema labarai na jaridar The Nation.

Daruruwan rayuka sun salwanta tare da asarar dukiya mai tarin yawa ta biliyoyin nairori a sanadiyar wannan mummunan rikici da ke ci gaba da aukuwa a tsakanin kabilun Jukun da Tibi tsawon shekaru aru-aru.

Sai dai bayan aukuwar harin na baya-bayan nan, wani uban gayya na kabilar Tibi, Stephen Butu, ya yi kira ga al'ummarsa a kan su zauna lafiya tare da daukar dangana inda ya yi neman kada su mayar da martani.

Babu shakka a halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza samun sukuni yayin da aka huro masa wuta a kan tabbatar da kawo karshen rikicin da ke tsakanin kabilun Jikun da kuma Tibi a jihar Taraba.

A wata zanga-zanga da aka gudanar cikin Abuja a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, wasu 'yan asalin jihar Taraba da kuma wadanda lamarin ke ciwa tuwo a kwarya, sun nemi shugaban kasa Buhari da ya shiga tsakanin rikicin da ya janyo asarar rayukan mutane da dama tsawon shekaru aru-aru.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta ci kananan hukumomi 5 a birnin Yola

Cikin wata rubutacciyar wasika zuwa ga shugaba Buhari da sa hannun madugun masu zanga-zangar, Mike Msuaan da kuma Solomon Adodo, sun roki gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta dauki mataki a kan masu haifar da fitina da rashin zaman lafiyar al'umma a jihar Taraba.

Masu zanga-zangar sun bayar da shaidar cewa, a halin yanzu su kansu kabilun Tibi da Jukun sun kosa wajen ganin sulhu ya tabbata a tsakaninsu wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sun kuma nemi shugaban kasa Buhari da ya umarci dukkanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki wajen bankado masu hura wutar rikicin da ke tsakanin kabilun biyu wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru bila adadin.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng