Bayan Fashewar Wasu Makamai a Barikin Sojoji, An Ji Halin da Ake ciki a Maiduguri
- Majiyoyin tsaro sun ce an shawo kan fashewar da ta faru a Barikin Giwa, Maiduguri da misalin ƙarfe 1:30 na Asubahin Alhamis
- Gwamnatin Borno ta tabbatar da cewa gobarar da ta tashi a ɗakin ajiye makaman ta faru ne sakamakon tsananin zafin rana da ake yi
- Sanarwar gwamnatin jihar ta shaida cewa fashewar makamai aka samu a barikin sojin ba wai wani farmaki ne aka kawo daga waje ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an samu lafawar fashewar da ta auku a Barikin Sojoji ta Giwa da ke Maiduguri, kuma an shawo kan lamarin da Asubahin ranar Alhamis.
Legit Hausa ta ruwaito cewa tashin abubuwan fashewa a barin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna birnin Maiduguri a daren Alhamis.

Asali: Twitter
Fashewar makamai ta lafa a barikin sojoji
Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X cewa bincike ya gano tsananin zafin rana ne ya haddasa fashewar wasu makamai a cikin ɗakin ajiyar makamai na barikin sojojin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar tsaro ta ce jami’an agajin gaggawa, ciki har da masu kashe gobara na soja da sauran hukumomi, sun kwana suna aiki domin dakile gobarar.
“An shawo kan matsalar, tun da misalin ƙarfe 1:30 na safe aka dakile fashe-fashen. An ɗauki duk matakan kariya da suka dace,” inji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa:
“Ba hari ne aka kawo daga waje ba. Wannan iftila'i ne da ya faru sanadiyyar zafi mai tsanani a wani ɓangare na ɗakin adana makamai."
Sannan ya ruwaito cewa ba a samu asarar rai ba a lokacin da makamai ke fashewa, kuma kwanciyar hankali ya dawo a yankin da lamarin ya auku.
Gwamnatin Borno ta magantu kan gobarar
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da faruwar gobarar da ta tashi a Barikin Giwa da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025.
Gwamnatin ta bayyana hakane ne a cikin wata sanarwa daga hukumar kashe gobara ta jihar Borno, karkashin ma’aikatar yaɗa labarai da tsaro ta cikin gida, inji rahoton Leadership.
Sanarwar ta yi karin bayani kan abin da ya faru da cewa gobarar da ta tashi ta shafi ɗakin ajiye makamai, inda hakan ya janyo fashewar wasu makamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa haɗin gwiwar jami’an kashe gobara daga rundunar sojin Najeriya, hukumar kashe gobara ta kasa da ta jiha sun kai ɗauki cikin gaggawa kuma sun kashe gobarar.

Asali: Facebook
"Zafin rana ya jawo tashin gobarar" - Gwamnati
Sanarwar ta ja kunnen jama’a cewa akwai yiwuwar sauran makamai su ci gaba da fashewa a kusa da yankin, don haka a guji zuwa kusa da wajen.
“Binciken farko ya nuna cewa zafin rana mai tsanani da ake fuskanta a Maiduguri a wannan lokaci ne ya haddasa gobarar.
“Jami’an kashe gobara na ci gaba da zama a wurin domin tabbatar da cewa an dakile yaduwar gobarar da kuma kwantar da hankulan jama'a"
- Inji sanarwar.
'Bam' ya tashi a gonar sojoji da ke Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu mazauna Legas sun shiga cikin fargaba a ranar Litinin sakamakon tashin wani abu mai fashewa da ya auku a gonar sojoji da ke Ikeja.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar hakan, tana mai cewa lamarin bai munana sosai ba, kuma tuni an fara bincike don gano musabbabin fashewar.
Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru a gonar ba, domin a baya tashin wani bam a barikin ya yi sanadiyyar mutuwa da barna mai yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng