NAF za ta fara amfani da jirage marasa matuƙi don yaƙar ƴan bindigan Zamfara da Katsina

NAF za ta fara amfani da jirage marasa matuƙi don yaƙar ƴan bindigan Zamfara da Katsina

Shugaban hafsin sojojin saman Najeriya, Air Vice Marshall Sadique Abubakar ya ce za a samar da jirage marasa matuƙi, UAVs, domin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga a Katsina da Zamfara.

Shugaban sojin ya bayyana hakan ne yayin wata walima da aka shirya don bikin Babbar Sallah da sojoji a jihohin yankin arewa maso yamma kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina a jawabinsa ya yi iƙirarin cewa a halin yanzu ƴan sanda 30 ne kacal ke bawa ƙauyuka 100 tsaro a jihar.

NAF za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa don yaƙar ƴan bindigan Zamfara da Katsina
Jirgi mara matuki: Hoto daga Najeriya World
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

Masari ya ce adadin ƴan sandan ba zai wadatar su samar da tsaro a jihar ba inda ya ce gwamnatinsa na aiki don yin doka da zai bawa hukumomi a jihar damar yaƙar ƴan bindigan.

Ya ce "ɓata garin" sun saje da mutanen gari hakan yasa akwai wahalar banbance su daga sauran mutane.

"Wannan zai taimaka wa ƙoƙarin da ake yi na samar da tsaro a unguwanni tare da cike giɓin da akwai saboda ƙarancin ƴan sanda da a yanzu ƴan sanda 30 ke kulawa da ƙauyuka 100," a cewar tsohon Kakakin Majalisar.

"Ko da sojoji sun yi maganin ƴan bindigan, wasu ɓata garin na iya tasowa cikin ƙanƙanin lokaci su maye gurbinsu idan babu shugabanci da isashen tsaro.

"Ƴan bindigan sun saje da mutanen gari saboda haka wasu lokutan akwai wahala sojojin na NAF su banbance su daga mutanen gari ba tare da ƴin barna ba a lokacin da suka kai hari.

"Ƴa kuma zama dole mutanen gari su dena tallafa ɓata garin ko basu bayanai ko mafaka."

A wani labarin, wani karamin jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari ya yayin da ya ke kokarin tashi sama a hanyarsa ta zuwa kasar Australia a ranar Asabar kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Hatsarin jirgin saman ya tona asirin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da ke Melbourne kuma an kama mutane biyar da ake zargin suna da alaka da masu safarar kwayoyi a Italiya.

Jirgin kirar Cesna wadda aka cika makil da kilogram 500 na hodar-iblis wato koken ya fado kasa ne yayin da ya ke yunkurin tashi daga wani karamin filin jirgi da ke Papua New Guinea a ranar 26 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel