Matawalle Ya Yiwa Gwamna Dauda Martani kan Zargin Daukar Nauyin 'Yan Bindiga

Matawalle Ya Yiwa Gwamna Dauda Martani kan Zargin Daukar Nauyin 'Yan Bindiga

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya zargi magabacinsa, Bello Matawalle da ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar
  • Bello Matawalle wanda shi ne ƙaramin ministan tsaro na Najeriya ya fito ya yi martani kan zargin da gwamnan nasa
  • Matawalle ya musanta zargin tare da nesanta kansa da ayyukan ƴan bindiga sannan ya ce za a ɓata masa suna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani kan zargin ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Matawalle ya musanta zargin da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi masa kan cewa shi ne ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar.

Matawalle ya yiwa Dauda Lawal martani
Matawalle ya musanta zargin daukar nauyin 'yan bindiga Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Da yake maida martani kan zargin, Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnan ya saba zarginsa da ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi tsohon gwamnan da yake zargi da alaƙa da ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Bello Matawalle ya maida?

Ofishin kula da harkokin yaɗa labarai na ƙaramin ministan tsaron ne ya fitar da martanin tsohon gwamnan na jihar Zamfara.

Matawalle ya musanta zargin hannu a harkar ƴan bindiga a jihar, inda ya bayyana zargin a matsayin ƙage da ƙoƙarin ɓata masa suna.

"Yana da kyau a sani cewa ƙoƙarin da ƙaramin ministan ya yi a lokacin da yake gwamnan Zamfara a tsakanin 2019 zuwa 2023, ya sanya aka rage matsalar ayyukan ƴan bindiga da sauran laifuffuka."

- Ofishin yaɗa labaran Matawalle

Karanta wasu labaran kan Matawalle

Kara karanta wannan

Dattawan Zamfara sun ba Gwamna Dauda shawara kan Matawalle

Matawalle: An ba Gwamna Dauda shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar dattawan Zamfara ta Zamfara ta yi kira da babbar murya ga mai girma gwamnan jihar, Dauda Lawal.

Ƙungiyar ta buƙaci Dauda Lawal da mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng