Bidiyon Matashi Da Aka Kama Bisa Zargin Kashe Mahaifinsa a Kano Bayan Caka Masa Wuka

Bidiyon Matashi Da Aka Kama Bisa Zargin Kashe Mahaifinsa a Kano Bayan Caka Masa Wuka

  • Jami’an Civil Defence a jihar Kano sun damke wani matashi da ake zargi da hallaka mahaifinsa
  • An rahoto cewa matashin dai kwakwalwar sa ta samu matsala sakamakon shan muggan kwayoyi
  • Tuni aka fara shirye shiryen mayar da gawar mahaifin Katsina domin yi masa sutura, inda aka mika matashin hannun yan sanda

Jihar Kano - Jami’an tsaro na Civil Defence a jihar Kano, sun kama wani matashi mai suna Alkasim Ya’u, bisa zarginsa da hallaka mahaifinsa.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Yola dake yankin karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

NDCDC ta kama matashin da ya kashe mahaifinsa a Kano
“Aljanna zai shiga ba hisabi”, In ji matashi da ya kashe mahaifinsa Kano Hoto: @official_NSCDC
Asali: Twitter

Babban kwamandan rundunar tsaron ta civil defence Mohammed Falala ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da manema labarai a Lahadi, 7 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Yadda matashi ya hallaka mahaifinsa a Kano, NSCDC

Falala ya ce lamarin ya faru ne a daren Juma’a da misalin karfe 1:30 na dare. a gidan marigayin mai suna Alhaji Salisu Bala, mazaunin unguwar Tudun Yola ‘C’, rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Falala:

“Marigayin Alhaji Ya’u Mohammed ya kai dansa asibitin kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Dawanau, domin duba lafiyarsa, kuma anan aka samu damar yi masa tanadin ganin Likita a ranar Asabar 6 ga watan Junairu."

Ya kara da cewa maimakon marigayin ya koma Katsina kamar yadda ya tsara, sai ya yanke shawara kwana a wajen dan’uwansa kafin washe gari su tafi ganin Likitan.

Ya ci gaba da cewa:

“Binciken mu ya nuna mana cewa matashi Alkasim na fama da tabun kwakwalwa sakamakon yawan shan kayan maye da yake.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

“Bayan zuwansu Tudun Yola ne sai dan ya samu wani makami tare da dabawa mahaifinsa, wanda da kyar jami’an mu suka kwace shi daga hannun matashin tare da garzayawa da shi zuwa Asibiti da kuma kama matashin.”

Ya kara da cewa yanzu haka yan’uwan mamacin na shirye shiryen daukar gawarsa zuwa jihar Katsina domin yi masa jana’iza tare da binne shi, yayin da shi kuma matashin suka mika shi hannun jami’an yan sanda na rijiyar zaki domin fadada bincike da kuma daukar matakin gaba.

Mahaifina yana aljannah, matashi

Da aka tambaye shi kan abun da ya yi wa mahaifinsa, matashin ya ce shi mahaifinsa na Aljannah inda ya bayyana kansa a matsayin dan wuta.

Kalli bidiyon a kasa:

Matashi ya sheke mahaifinsa a Kaduna

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wani matashi dan shekaru 20, David Felix, ya kashe mahaifinsa kan cewa yana zuwa masa a cikin mafarki.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, matashin ya aikata laifin ne a gidansu da ke kauyen Madakiya, karamar hukumar Zango-Kataf ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel