Abu Ya Yi Zafi: Akwai Yiwuwar Ta'adi, Kwamandojin Ƴan Bindiga Sun Gana a Zamfara

Abu Ya Yi Zafi: Akwai Yiwuwar Ta'adi, Kwamandojin Ƴan Bindiga Sun Gana a Zamfara

  • Majiyoyi sun bayyana cewa shahararrun 'yan bindiga sun gudanar da wata muhimmiya ganawa a dajin yamma da Kaura Namoda a Zamfara
  • Ana gudanar da taron ne a gidan wani basaraken Fulani da ake kira “Sarkin Fulani,” wanda ke cikin daji a yankin na jihar Zamfara
  • Majiyar ta bayyana taron a matsayin ganawar manyan kwamandojin kungiyoyin bindiga daga Zamfara, Sokoto, Katsina da wasu sassan Kebbi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ƙaura Namoda, Zamfara - Rahotanni da muka samu sun tabbatar da cewa wasu manyan yan bindiga sun gana a jihar Zamfara.

Majiyoyi suka ce mayaƙan sun taru ne a wani daji da ke yankin karamar hukumar Kaura Namoda a jihar.

Manyan yan bindiga sun yi taro a dajin Zamfara
Wasu kwamandojin ƴan bindiga sun yi ganawa a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Shafin Zagazola Makama ya tabbatar da haka a daren yau Asabar 3 ga watan Mayun 2025 a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji ke murkushe ƴan bindiga

Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojoji na ci gaba da murkushe yan bindiga da suka addabi wasu yankuna a jihar Zamfara.

Dakarun Runduna ta 1 a Najeriya sun hallaka manyan ‘yan bindiga a Zamfara, ciki har da Auta Jijji da Dankali a kokarin yaki da ta’addanci.

An ce sojoji sun fafata da ‘yan bindiga a kauyen Mai Kwanugga a Talata-Mafara, inda suka kwato bindigogi da makamai masu linzami bayan kashe su.

A wani lamari daban a Dayau, Kaura-Namoda, sojoji da ‘yan sanda sun shawo kan tarzoma da mazauna suka ta da saboda harin ‘yan bindiga a yankin.

An samu bayanai game da ganawar manyan yan bindiga a Zamfara
Kwamandojin ƴan bindiga sun yi wata ganawa a dajin Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Kwamandojin ƴan bindiga sun yi wata ganawa

Wasu na ganin ganawar mayakan bai rasa nasaba da yawan kisan jagororinsu da ake yi kusan kullum musamman a Arewacin Najeriya.

Wata majiya ta leken asiri ta bayyana cewa wasu shahararrun 'yan bindiga na gudanar da taron ne mai muhimmanci a dajin yamma da Kaura Namoda.

A cewar wata majiya mai karfi, ana gudanar da wannan ganawa ne a gidan wani basaraken Fulani da ake kira “Sarkin Fulani” a cikin daji.

An bayyana wannan ganawa a matsayin taron manyan kwamandojin kungiyoyin 'yan bindiga da ke aiki a Zamfara, Sokoto, Katsina da sassan Kebbi.

Martanin wasu ƴan Najeriya kan rahoton

Wasu yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan ganawar inda suke cewa ta yaya ba za a jefa bam kan miyagun a karar da su ba gaba ɗaya.

@IdrisAOni1:

"Wannan Sarki din, dan Najeriya ne ko dai daga ketare yake?"

@Abdul_A_Bello:

"Ku yi amfani da jirgi marar matuki ku jefa bam a wurin, shin wannan abu ne mai wahala wurin aiwatarwa?"

@adeyanjuayodej6:

"Ta yaya kuka samu wannan bayani amma jami'an tsaronmu ba su gano haka ba, ina fatan za a ɗauki tsattsauran mataki."

Ƴan bindiga sun hallaka limami a Zamfara

A wani labarin mai kama da wannan, 'yan bindiga sun kashe wani babban limami, Malam Salisu da wasu 'yan uwansa biyu da suka yi garkuwa da su wata biyu baya.

Malam Salisu da yan uwansa sun kasance a hannun 'yan bindigar ne tun wata biyu da suka gabata kafin a yi ajalinsu.

Lamarin ya tayar da hankulan al'ummar yankin da ke Zamfara da kara jefa al'umma cikin fargaba da bakin ciki a yankunan da ake fama da rikici.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.