Kungiyar Kiristocin Najeriya Ta Dare Gida 2, An Samu Hatsaniya kan Seyi Tinubu
- An samu sabani a tsakanin shugabannin kungiyar Kiristoci (CAN) bayan wasu rahotanni da suka danganta Seyi Tinubu da tarwatsa taron NANS
- Shugaban CAN na Arewa ya kare Seyi, yana mai cewa bai kama a zarge shi da laifin da bai aikata ba saboda saboda mahaifinsa ne shugaban kasa
- Sai dai, shugaban CAN na ƙasa, Archbishop Daniel Okoh, ya kalubalanci Hayab, yana mai cewa ba shi da hurumin yin wannan magana a madadinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Akwai alamun rabuwar kai a tsakanin shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) dangane da wasu rahotannin da suka shafi Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu.
Wasu kafofin yada labarai sun wallafa cewa 'yan daba da ke da alaƙa da Seyi Tinubu sun tarwatsa bikin rantsar da shugabannin wani tsagi na ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS).

Asali: Twitter
Martanin shugaban CAN na Arewa
Rahotannin sun kuma nuna cewa wasu fitattun 'yan Najeriya, ciki har da tsofaffin gwamnoni biyu; Sanata Ibrahim Shekarau na Kano da Kyaftin Idris Wada na Kogi na cikin wadanda aka farmaka, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan lamari ya sa Reverend John Joseph Hayab, shugaban CAN na jihohin Arewa 19 da Abuja, ya fito ya karyata rahotannin, yana mai cewa ba daidai ba ne a ci zarafin Seyi Tinubu da ƙage kawai don shi ɗan shugaban ƙasa ne.
A wata sanarwa da ya sanya hannu da kansa, Hayab ya ce bai dace a ɗora wa Seyi laifi ko a ƙirƙiri labaran ƙarya kawai saboda mahaifinsa ne shugaban ƙasa ba.
Shugaban CAN ya nesanta kansa da Hayab
Amma kuma, cikin gaggawa, shugaban CAN na ƙasa, Archbishop Daniel Okoh, ya nesanta kungiyar daga maganganun Hayab, yana mai cewa shugaban CAN na kasa ne kadai ke da ikon fitar da wata sanarwa ta ƙasa ko ta ƙasa da ƙasa.
Ya bayyana cewa wannan gyara yana da muhimmanci don kare sahihancin matsayin CAN da kuma dakile yaɗuwar bayanan da ba su da tushe.
Okoh ya ce CAN na da tsarin matakai huɗu, kuma matakin ƙasa ne ke da hurumin tsara manufofi da fitar da matsayinta kan wani abu da ke faruwa.
Punch ta rahoto Okoh ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin CAN ya tanadar da cewa shugaban kungiyar na kasa ne kaɗai ke da ikon fitar da wata sanarwa a madadin CAN a hukumance.
“Duk wani sashen CAN a matakin yanki, jiha ko ƙaramar hukuma, ba su da hurumin fitar da wata sanarwa da za a ɗauka a matsayin matsayar kungiyar ta kasa, sai an ba su izini daga uwar kungiya."
- Archbishop Daniel Okoh.

Asali: Facebook
CAN ta yi gargadi ga kafafen yaɗa labarai
Archbishop Okoh ya ce ya samu labari cewa ana yaɗa wasu rahotanni daga kungiyoyi irin su ‘CAN Arewa’ da ‘CAN Kudu’ da sauran kungiyoyin da ba su da iko a hukumance, yana mai cewa CAN ba ta amince da irin waɗannan rassa ba.
Shugaban kungiyar na kasa ya ce irin wadannan rahotanni ba su da inganci kuma ya kamata jama'a da kafafen labarai su yi watsi da su.
Archbishop Okoh ya roƙi kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin kowace sanarwa da ake dangantawa da CAN ta hanyar tuntuɓar ofishin sakatariyar ƙasa don tabbatar da cewa shugaban kungiyar na kasa ko wakilinsa ne ya sanya hannu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen hana yaɗuwar ƙarya da kuma kiyaye martabar CAN a idon duniya.
Ana so Seyi Tinubu ya nemi gwamnan Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gamayyar kungiyoyin matasa ta CONYL ta bayyana goyon bayanta ga Seyi Tinubu ya zama gwamnan jihar Legas.
Gamayyar kungiyar CONYL ta ce lokaci ya yi da Seyi, ɗan Shugaba Bola Tinubu, zai bi sawun mahaifinsa ta hanyar tsayawa takarar gwamna a zaben 2027.
Kungiyoyin daga shiyyoyi shida na Najeriya sun bayyana cewa suna da yakinin Seyi zai kawo cigaba da dorewar tafiyar siyasa a Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng