Kungiyar CAN Ta Bukaci Mazauna Jihar Kaduna Su Kare Kawunansu Daga Hare-haren 'Yan Bindiga

Kungiyar CAN Ta Bukaci Mazauna Jihar Kaduna Su Kare Kawunansu Daga Hare-haren 'Yan Bindiga

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta yi kira ga mazauna jihar su kare kawunansu
  • Ƙungiyar ta CAN ta bayyana cewa matsalar tsaro wata aba ce da ta shafi kowa da kowa a halin da ake ciki
  • Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Kaduna, John Hayab ne ya bayyana hakan bayan wani hari da aka kai a Kafanchan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta yi kira ga mazauna kudancin Kaduna da ma sauran garuruwan da ke jihar baki daya da su tashi tsaye wajen kare kawunansu daga hare-haren 'yan ta'adda.

Shugaban kungiyar CAN na jihar Kaduna, John Joseph Hayab ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan harin da 'yan bindigan suka kai a wata coci da ke Kafanchan, ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Wurin Ibada a Jihar Kaduna, Sun Kashe Malami

Kungiyar CAN ta bukaci mazauna Kaduna su kare kawunansu
Kungiyar CAN shawarci mazauna Kaduna su kare kawunansu daga hare-haren 'yan bindiga. Hoto: John Joseph Hayab
Asali: Facebook

Ƙungiyar CAN ta bukaci mazauna Kaduna su kare kawunansu

John Hayab ya ce matsalar tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa ta yanda ya zama wajibi jama'a su tashi tsaye wajen kare yankunansu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira ga gwamnan jihar Kaduna da ma sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaron jihar Kaduna da su tabbatar da cewa an gano wadanda suka aikata ɗanyen aikin domin su fuskanci hukunci.

Ya ce abin kunya ne ga jami'an tsaro, malaman addini, shugabanni na gargajiya da ma sauran shugabannin garin Kamantan da mummunan lamarin ya faru.

Ya jinjinawa Uba Sani bisa daukar 'yan sa kai 7,000

John Hayab ya kuma bayyana cewa matsayar ƙungiyar CAN ta jihar Kaduna a kodayaushe ita ce kira ga al'umma da su bai wa gwamnati haɗin kai wajen tabbatar da tsaron yankunansu.

Kara karanta wannan

"Babu Dawowa Baya", Kashim Shettima Ya Tona Asirin Shirin Masu Handame Kudaden Tallafi, Ya Tura Gargadi

Ya jinjinawa Gwamna Uba Sani bisa yunƙurin daukar 'yan sa kai maza da mata sama da 7,000 da yake shirin yi, inda ya ce hakan shi ne abinda ya fi dacewa wajen yaƙi da ta'addancin da ya addabi jihar.

Hayab ya kuma jaddada bukatar shugabannin al'ummar yankin Kudancin Kaduna na su tashi tsaye wajen ganin sun yi amfani da wannan damar don samar da tsaro a yankunansu.

'Yan bindiga sun kashe mutane 2, sun dauke 11 a Kaduna

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani hari da 'yan bindiga suka kai garin Jere da ke jihar Kaduna, inda suka halaka mutane 2 gami da yin awon gaba da wasu 11.

Mazauna garin na Jere sun koka cewa jami'an tsaro ba su kawo mu su ɗauki ba duk kuwa da yunƙurin sanar da su da wuri da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel