'Ku Gyara Aikinku': Jingir Ya Yi Alhinin Gobara a Jos, Ya Shawarci Hukuma
- Shugaban Majalisar malamai a kungiyar Izalah, Muhammad Sani Yahya Jingir ya nuna alhini kan gobarar da ta tashi a kasuwar Taminus da ke Jos
- Shehin ya yi addu’ar Allah SWT ya kiyaye gaba, sannan ya roƙi gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa wa waɗanda suka yi asara
- Sheikh Jingir ya buƙaci hukumar kashe gobara ta duba matsalolinta tare da gyara domin a guji sake fuskantar irin wannan masifar nan gaba
- Ya ƙara da addu’a cewa Allah Madaukakin Sarki ya mayar da asarar da aka yi ta zama kaffara ga duk wanda ya rasa dukiya dalilin gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Shugaban majalisar malamai, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya magantu game da gobara a babbar kasuwar Jos.
Shehin malamin ya bayyana jimami da tausayi game da gobarar da ta afku a kasuwar 'Taminus' da ke Jos.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Jibwis Gombe State ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mummunar gobara ta laƙume shaguna a Jos
Ta'azziyar Sheikh Jingir na zuwa ne bayan gobara ta lakume shaguna da runfuna da dama a babbar kasuwar Terminus a garin Jos da ke Plateau.
An ce gobarar ta yi sanadin asarar dukiya mai yawa kamar yadda wasu daga cikin 'yan kasuwar suka shaidawa yan jaridu a jihar Plateau.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa gobarar ta ci runfunan 'yan kasuwa da yawa wadanda har yanzu ba a iya sanin adadin asarar da aka yi ba.
Rahotanni sun ce ce har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, saboda a cikin tsakiyar dare iftila'in ya afku ba da ranar Allah ba.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Undie Adie ya nuna damuwa kan lamarin, ya ce bayan samun labari sun sanar da jami'an kashe gobara domin takaita lamarin.
Gobarar Jos: Abin da Sheikh Jingir ya ce
A cikin sanarwar, Sheikh Jingir ya nuna alhininsa kan abin da ya afku, ya bukaci gwamnatin jihar ta tallafa musu.
Ya roƙi Allah ya kare faruwar irin wannan iftila'in a gaba, yana mai kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni su tallafa wa waɗanda suka yi asara.
Jingir ya kuma buƙaci hukumar kashe gobara ta duba ayyukanta tare da yin gyara domin guje wa irin wannan matsala a gaba.
A ƙarshe ya yi addu’a cewa Allah ya mayar da abin da aka rasa ya zama kaffara ga duk wanda ya samu asara a gobarar da ta faru.
Sheikh Jingir ya yabawa Gwamna Caleb Mutfwang
A baya, kun ji cewa Shugaban kungiyar Izalar Jos, Sani Yahaya Jingir ya yabawa gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang bisa kokarin da yake yi a ɓangarori uku.
Sheikh Jingir ya ce gwamnan yana matuƙar kokari wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da kuma gudanar da mulkin adalci a Plateau.
Malamin ya yi wannan yabon ne da Gwamna Mutfwang ya kai masa ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar Sheikh Sa'eed Hassan Jingir.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng