Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria

- Gobara ta lashe dakuna a barikin sojoji na Nigerian Army Depot da ke Zaria a Jihar Kaduna

- Wasu shaidun ganin ido sun ce tun tsakar daren ranar Asabar gobarar ta tashi amma ana can ana kokarin kashe wuta

- A halin yanzu babu tabbas a kan adadin abinda aka yi asara sakamakon gobarar

Gobara ta tashi a barikin sojojin Najeriya da ke Zaria a Jihar Kaduna inda ta lalata wasu kadarori, Premium Times ta ruwaito.

Ba a tabbatar ko gobarar ta yi sanadiyar rasa rayyuka ba a lokacin hada wannan rahoton a yayin da ake kokarin kashe gobarar.

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria. Hoto: Premium Times
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

Ana amfani da barikin ne domin horas da sabbin sojojin da aka dauka.

Kazalika, akwai makarantar sakandare ta sojoji wato Nigerian Military School da wasu makarantun na frimare da sakandare a cikin barikin.

Tun bayan kafa barikin a shekarar 1924, ana amfani da shi wurin bawa sojoji horo.

A cewar wasu wanda abin ya faru a idonsu, gobarar ta da fara tsakar daren ranar Asabar ta kone wasu dakuna a Block 15 na gidajen sojoji.

KU KARANTA: Hotuna: An fatattaki Sarkin Fulanin Oyo da iyalansa daga gidansa, an ƙone motocinsa 11

An yi kokarin ji ta bakin jami'an sojoji daga barikin amma hakan bai yi wu a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel