Neja: Yadda Wani Bawan Allah Ya Rasa Matarsa sakamakon Dauke Wutar Lantarki a Asibiti
- Wani Bawan Allah dan Najeriya ya bayyana yadda ya rasa matarsa sakamakon daukar wutar lantarki yayin da ake yi mata tiyata a asibiti
- Ya bayyana cewa janaretan asibitin bai da mai a lokacin da wutar ta dauke, kuma ya bayyana abin da ya faru bayan daga bisani aka kawo fetur
- Mutane da dama da suka ga wallafar tasa sun nuna alhinin su tare da yi masa ta’aziyya, suna addu’ar Allah ya jikanta ya sa ta huta lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Wani Bawan Allah a Najeriya, UB Shehu ya bayyana yadda ya rasa matarsa bayan an dauke wutar lantarki yayin da ake tsaka da yi mata tiyata.
Ya bayyana sunan asibitin da abin ya faru, inda ya rika wallafa jerin sakonni kan abin da ya faru bayan wutar ta dauke a lokacin tiyatar.

Asali: Facebook
A jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, UB Shehu ya ce lamarin ya faru ne a Babban Asibitin Jummai Babangida Aliyu dake jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda baiwar Allah ta rasu a Neja
Magidancin, a cikin takaici da sallamawa Allah Subhanahu wa ta'ala komai, ya bayyana cewa mintuna 35 bayan an fara yi wa matarsa aiki ne sai aka dauke wuta.
Ya wallafa cewa:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Na rasa matata. Mintuna 35 da fara tiyata sai NEPA suka dauke wuta, babu mai a janaretan dakin tiyata a Asibitin Jummai Babangida Aliyu.
Bayan an kawo mai, janareto ya ki aiki. Sai aka kira me gyara, amma har lokacin, matata tana cikin dakin tiyata."
Ya kara da cewa daya daga cikin masu jinya a dakin tiyata ta ce masa kada ya damu domin an ci gaba da aikin tiyatar da hasken ko fitila kamar yadda suka saba.
Ya ce:
"Me gyara ya iso, amma akwai wasu kayayyaki da ya ce sai ya je yankin Ogbomosho a Minna domin siyo su. Matata har yanzu tana cikin dakin tiyata."
An dawo da wuta a asibitin a Neja
Ya bayyana cewa bayan awa daya da faruwar lamarin, wuta ta dawo amma me gyaran na cigaba da kokarin gyaran janareto.

Asali: Facebook
Ya kara da cewa:
"Tiyatar da ba za ta wuce mintuna 90 ba, ta dauki lokaci daga 4.00 zuwa 7.00 na dare. Na jira tsawon awa 11 daga karfe 8:44 na safe har zuwa 7:00 na dare."
TCN ta yi magana kan rashin wuta
A baya, kun samu labarin cewa Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya bayyana halin da ake ciki bayan katsewar wutar lantarki da ta shafi yankin Arewa na tsawon lokaci.
A cewar sanarwar, kamfanin ya ce daga lokacin da aka samu matsalar katsewar wutar, nan da nan suka tura injiniyoyi domin su gano matsalar da da zummar kawo karshen matsalar.
Al’umma a wasu sassan Arewa sun shiga duhu a watannin baya, lamarin da ya jawo koke-koke daga mutane da dama da kuma tasiri ga harkokin yau da kullum, ciki har da kasuwanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng