'Dan Majalisar Kano, Ya Buɗe Shirin Tallafin Karatu, Zai Tura Dalibai Kasashen Waje
- An buɗe zagaye na biyu na shirin tallafin karatu na kasashen waje, wanda aka ware musamman ga dalibai mata 'yan asalin karamar hukumar Bichi
- 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Bichi ne ya bude guraben karatun, kuma an fara karbar bayanan daliban ta yanar gizo
- Wannan dama ce ga matan da suka kammala digiri domin su ci gaba da karatu a ƙasashen waje a fannonin da ke da muhimmanci ga ci gaban yankinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano – Ofishin mai ba da shawara na musamman kan shirin tallafin karatu na kasashen waje na ɗan majalisar Bichi, Abubakar Kabir Bichi zai dauki nauyin karatun dalibai mata.
Ofishin ya sanar da cewa an buɗe zagaye na biyu na ɗaukar nauyin daliban ne domin su zurfafa ilimi a kasashen waje, a fannonin da za su ciyar da su da al'ummar Bichi gaba.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mashawarcin ɗan majalisar kan tallafin karatu na kasashen waje, Mukhtar Nura Bichi, ya fitar, wadda aka wallafa a shafin Facebook na Hon. Abubakar Kabir Abubakar.
'Dan majalisa ya buɗe kofar tallafa wa dalibai
A wata tattaunawa da Legit, Honorabul Mukhtar Nura Bichi ya tabbatar da cewa wannan shi ne zagaye na biyu na shirin tallafin karatun kasashen waje na Bichi, kuma na mata ne kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa an fara karɓar buƙatun neman guraben karatu daga ranar 28 ga Afrilu, kuma za a rufe karɓar buƙatun a ranar 4 ga Mayu, 2025.
Ya ce:
"Ba a fara tantance su ba; yanzu nema ake yi. Bayan kammala karɓar bayanan masu neman a ɗauki nauyin karatunsu, za mu duba yawan daliban da muka samu da kuma abin da suka karanta a digirinsu na farko."

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa ɗan majalisar zai ɗauki nauyin daliban ne domin su yi karatu a fannonin kimiyya da fasaha waɗanda ba su da yawa a Najeriya.
Dalilin ɗan majalisar na taimakon daliban Bichi
Mukhtar Nura Bichi ya bayyana cewa sha'awar Honorabul na inganta rayuwar matasa ne ya sanya shi ke ɗaukar nauyin karatun dalibai.
Ya ce:
"Tun asali, babban abin da Honorabul ya mayar da hankali a kansa shi ne harkar ilimi."
"Tun daga matakin firamare, sakandare, har zuwa gaba da sakandare — jami'a da kwalejin ilimi — yana ɗaukar nauyin kuɗin makaranta kyauta ga daliban karamar hukumar Bichi."
Ya ce wannan mataki na daga cikin cika alkawarin da ɗan majalisar ya ɗauka cewa zai ci gaba da tura dalibai zuwa kasashen waje idan aka sake zabensa.
'Dan majalisar Dala ya shiga matsala
A wani labarin, kun ji cewa yunƙurin sauke mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini, ya ƙara ƙamari a mazabarsa ta Dala da ke jihar Kano.
Rahotanni sun ce jiga-jigan siyasa a Kano ne ke jagorantar wannan yunƙuri, ciki har da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokokin Kano, Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yar Gurasa.
A cewar waɗanda ke goyon bayan kiranyen, ɗan majalisar ya ci amanar jam’iyyarsa ta NNPP da kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng