Da Gaske Gwamnonin APC 5 Za Su Koma Tafiyar Atiku? Gwamna Buni Ya Yi Magana

Da Gaske Gwamnonin APC 5 Za Su Koma Tafiyar Atiku? Gwamna Buni Ya Yi Magana

  • Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce ba zai shiga kawancen 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ba a siyasance
  • Wani saƙo da ya bazu ya yi zargin cewa Buni da wasu gwamnoni hudu na APC sun shirya sauya sheka zuwa PDP kafin 2027
  • Daraktan yaɗa labarai, Mamman Mohammed, ya karyata zargin, yana cewa Buni babban ɗan APC ne kuma gudunmuwarsa ga jam’iyyar ba za a musanta ba
  • Mohammed ya ƙara da cewa masu yaɗa jita-jitar suna mafarkin samun irin ƙwarewar Buni a siyasa, amma hakan mafarki ne kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi martani kan jita-jitar barin jam'iyyar APC.

Gwamna Buni ya ƙaryata labarin cewa zai shiga kawancen shugabannin adawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Gwamna Buni ya magantu kan zargin komawa tafiyar Atiku
Gwamna Mai Mala Buni ya musanta shirin shiga tafiyar Atiku Abubakar. Hoto: Hon. Mai Mala Buni.
Asali: Facebook

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai, Alhaji Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu ranar Asabar, cewar vangaren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 5 da ake yada za su bar APC

Rahotanni sun ruwaito cewa wani saƙon waya da ya bazu ya ce Buni da wasu gwamnoni hudu za su koma PDP.

Majiyoyin suka ce gwamnoni hudu na APC sun hada Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe da Alia Hyacinth na Benue da ke Arewacin Najeriya.

Sai kuma Kwamred Nasir Idris na jihar Kebbi da takwaransa na Niger, Mohammed Umar Bago da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Sannan rahoton ya yi zargin cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ma zai bar APC idan har ba a ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a matsayin mataimaki ba.

Gwamna ya ƙaryata labarin zai bar APC zuwa tafiyar Atiku
Gwamna Buni na Yobe ya musanta shirin barin APC domin tafiyar Atiku Abubakar. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

Martanin Gwamna Buni kan jita-jitar barin APC

Mohammed ya bayyana saƙon da ya bazu a matsayin ƙirƙira mara tushe da mafarki marar tushe da bai da wata alaƙa da gaskiya.

Ya ce marubucin saƙon bai taɓa kusantar gwamna Buni ba, balle ya iya hasashen shirin siyasar gwamnan cikin wani yanayi.

A cewarsa:

"Buni ba ɗan APC na yau da kullum ba ne; ba kawai gwamna na APC ba ne. APC ta na gudana a cikin jininsa.
"Gudunmuwar da ya bayar wajen gina APC a matsayin Sakataren Ƙasa da Shugaban rikon kwarya ya bambanta shi, ba za a iya hasashe zai fita ba."

Mohammed ya ce marubucin saƙon da masu ɗaukar nauyinsa aka yi wanda suke mafarkin samun irin ƙwarewar siyasa da Gwamna Buni ke da ita.

Ya ce:

"Wannan mafarki ne kawai."

Ɗan APC a Gombe ya fadi ra'ayinsa

Wani ɗan a mutum APC a Gombe, Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya kan zargin Inuwa zai koma PDP.

"Sakataren yada labaran gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya ƙaryata labarin kua babu wanda zai yarda Inuwa zai yi haka."

- Cewar Ibrahim

Ya bukaci masu yada jita-jita da su san irin gwamnonin da za su danganta da irin haka amma ba Inuwa Yahaya ba.

Fasto ya yi magana kan zaben 2027

Kun ji cewa shugaban coci na INRI, Rabaran Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa gwamnoni hudu na PDP za su mara wa APC baya a zaben 2027.

Ayodele ya bayyana jihohin Akwa Ibom, Enugu, Oyo da Osun a matsayin wuraren da za a shawo kansu su sauya zuwa jam'iyyar APC.

Faston ya ce babu wani abu da ake kira kungiyar PDP yanzu, domin dukkan gwamnoni za su yi aiki ne da APC ba tare da shakka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.