An Yi Harbe Harben Bindiga a wajen da ake Gangamin Goyon bayan Wike

An Yi Harbe Harben Bindiga a wajen da ake Gangamin Goyon bayan Wike

  • An samu rikici da harbe-harbe a wurin taron magoya bayan ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, a Yenagoa, jihar Bayelsa ranar Asabar
  • Taron da ƙungiyar NEW Associates ta shirya ya ci gaba duk da harbe-harben, inda magoya baya suka sake haɗuwa domin ci gaba da gangamin
  • Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya ce gwamnati ta hana taron tun farko domin gudun ya haddasa rikici kamar yadda ke faruwa a jihar Ribas

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bayelsa - Harbe-harbe ya tayar da hankula a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, yayin da ake gangamin girmamawa ga tsohon gwamnan Ribas kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rahotanni sun bayyana cewa taron ƙungiyar NEW Associates, ƙarƙashin jagorancin George Turnah, wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar, ya fara tafiya tafiya kafin a fara harbe-harbe.

Bayelsa
An yi harbe harbe wajen taron Wike a Bayelsa. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike.
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa an shawo kan lamarin, inda aka tabbatar da dawowar zaman lafiya, kuma magoya bayan kungiyar sun cigaba da gudanar da taronsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cigaba da gangamin Wike a Bayelsa

Bayan aukuwar harbe-harben, sakataren ƙungiyar NEW Associates a Bayelsa, Kwamred Ebilade Ekerefe, ya bayyana wa manema labarai cewa taron zai ci gaba kamar yadda aka tsara.

Magoya bayan ƙungiyar sun sake haɗuwa domin ci gaba da nuna goyon bayansu ga Wike, duk da ɗan tashin hankalin da aka samu a daidai lokacin.

Wannan lamari ya nuna irin jajircewar magoya bayan Wike da ƙungiyar wajen ganin an cika manufar taron duk da kalubalen da suka fuskanta.

Gwamnatin Bayelsa ta hana taron Wike

Premium Times ta wallafa cewa gwamnatin jihar Bayelsa ta sanar da dakatar da taron tun kafin a gudanar da shi domin kauce wa rikice-rikicen siyasa.

Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa gwamnati na da niyyar kare zaman lafiyar jihar, ganin yadda rikicin siyasa ke ci gaba da ta'azzara a jihar Ribas.

Diri ya jaddada cewa gwamnatinsa na mutunta ‘yancin jama’a bisa kundin tsarin mulki, amma ana buƙatar yin taka tsantsan a irin wannan lokaci mai sarkakiya.

Douye Diri
Gwamnan Bayelsa ya hana taron Wike a jiharsa. Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Tasirin taron Nyesom Wike a siyasar Neja Delta

Masu fashin baki sun bayyana cewa lamarin wata alama ce ta zurfafa sabani a tsakanin ‘yan siyasa na Kudu maso Kudu.

Har yanzu dai ana sa ido kan yadda abubuwa za su kaya, musamman ganin yadda lamarin siyasar Ribas ke da tasiri kan makwabtan jiharsa kamar Bayelsa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu sanarwa kan wadanda suka yi harbe harben ba kasancewar gwamnati bata yi magana ba.

Wike ya yi magana kan zaman lafiya a Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan zaman lafiya a Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa Nyesom Wike ya fitar da sharudan da ya ce idan aka bi su za a samu zaman lafiya a jihar.

Hakan na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da aka yi tsakanin Bola Tinubu da gwamna Simi Fubara da aka dakatar a Maris.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng