Gwamnati Ta Gurfanar da babban Sarki a Kotu, Ana Zargin Ya Kwace Filayen Mutane

Gwamnati Ta Gurfanar da babban Sarki a Kotu, Ana Zargin Ya Kwace Filayen Mutane

  • Gwamnatin Ogun ta gurfanar da sarkin Obafemi, Oba Taofeek Owolabi a kotu bisa zargin kwace da sayar da fili ba bisa ka’ida ba
  • An ce sarkin ya sayar wa wani mutumi wata gona a kan ₦75m, amma ya ki ba masu gonar kuɗinsu, sai ma ya tura masu 'yan daba
  • Duk da gayyatar majalisar dokokin jihar da majalisar sarakunan gargajiya, Oba ya ƙi mika wuya, lamarin da ya kai ga gurfanar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta ce ta gurfanar da Sarki Taofeek Owolabi, a gaban kotu bisa zargin kwace filaye ba tare da izini ba.

An gurfanar da Sarkia Owolabi, wanda ke cikin majalisar sarakunan Egba a ranar Talata yayin da gwamati ta dakatar da mukaminsa.

Gwamnatin Ogun ta gurfanar da Sarki Taofeek kan kwacen fili da farmakar dan sanda
Sarki Taofeek Owalabi (Hagu), Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun. Hoto: @OGSG_Official
Asali: Twitter

An gurfanar da basarake kan kwacen fili

Ma’aikatar shari’a a ranar Laraba, ta ce gwamnati ta gurfanar da basaraken ne bisa zargin haɗa baki don siyar da filayen jama'a ba tare da izini ba, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran laifuffukan sun haɗa da siyar da fili ba bisa ka'ida ba, amfani da wakilai ba bisa ƙa'ida ba, kwace fili da ƙarfin tsiya, dukan ɗan sanda, da kuma karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

Sanarwar ta ce ana zargin Oba Owolabi da ikirarin mallakar wata gona mai fadin eka 500 a garin Obafemi Owode, inda ya yaudari wani Dakta Michael Adeyemi, ya karɓi ₦75m daga hannunsa.

An kuma ce bai mika kuɗin ba ga iyalan da ke da gonar ba, sai ma ya tura 'yan daba zuwa gonar suka sare wani mutum.

Haka kuma an ce basaraken da kansa ya kai hari kan wani ɗan sanda na tawagar hana kwacen filaye ta jihar Ogun.

Sarkin Obafemi ya ki amsa gayyatar majalisa

Gwamnatin jihar Ogun ta ce ta yi amfani da matakai da dama na tsawatarwa Oba Owolabi, ciki har da kiran da majalisar dokokin jihar ta yi masa a watan Yulin 2024.

Sai dai sanarwar ta ce basaraken ya ƙi amsa gayyatar majalisar jihar, maimakon hakan, sai ma ya kai ƙara kotu don kalubalantar hakan.

Sanarwar ta ce:

“Oba Owolabi daga baya ya janye ƙarar da ya shigar, amma bai bayyana a gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki ba, wanda daga bisani aka bayar da shawarar gurfanar da shi kan kwacen fili.”

Karkashin jagorancin sarkin sarakunan ƙasar Egba, HRM Oba Aremu Gbadebo, Alake na ƙasar Egba, an gayyaci Oba Owolabi sau da dama amma ya ƙi amsa gayyatar.

Gwamnatin Enugu ta gargadi masu kwacen filaye
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Enugu. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gwamnati ta gargadi masu kwacen fili a Ogun

Kwamitin ladabtarwa na majalisar sarakuna ta Egba ma ya tuntube shi amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba, lamarin da ya sa a ranar 13 ga Disamba, 2024, aka dakatar da shi daga sarautar Sarkin Obafemi.

Sanarwar ta bayyana cewa duk da cika sharuddan beli da Oba Owolabi ya yi, shari'arsa na ci gaba da gudana, kuma gwamnati ta yi alkawarin tabbatar da adalci.

“Gwamnatin jihar Ogun na tabbatar wa jama’a cewa za mu ci gaba da tsabtace harkar mallakar fili, kuma muna da ƙuduri na gurfanar da Oba Owolabi.”
“Matukar muna da iko da ikon yin hakan, za mu yi tsayin daka wajen hana kwacen fili, za kuma mu taka wa masu kwacen fili burki, komai girman matsayinsu.”

- Inji sanarwar.

Majalisa ta ba da shawarar gurfanar da sarki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar jihar Ogun ta amince da gurfanar da Sarkin Obafemi, Oba Taofeek Owolabi, bisa zargin hannu a rikicin kwace filaye a masarautarsa.

Majalisar ta bayyana cewa akwai hujjoji da ke nuna sarkin na da alaka da cin zarafin jami'in dan sanda, mallakar filaye ba bisa ka’ida ba da dai sauransu.

Daga ƙarshe, ta umurci ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu da kuma majalisar sarakunan jihar su dakatar da shi nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.