Wani Farfesan Najeriya Ya Kira Gwamnoni 'Masu Kwacen Filaye'

Wani Farfesan Najeriya Ya Kira Gwamnoni 'Masu Kwacen Filaye'

  • Wani farfesa na fannin sarrafa dukiya a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, Bioye Tajudeen Aluko ya kira gwamnonin Najeriya da masu kwace filaye
  • Yayin da yake jawabi a wani taron kara wa juna sani a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Aluko ya ce suna amfani da dokokin filaye wurin amsar filaye suna ba mutanensu
  • Babban malamanin yayin jawabin, ya ce gwamnonin suna da wata dabi’a ta azurta kawunansu da abokansu na siyasa ta hanyar kwace wa mutane filayensu

Ogun - Wani farfesa tsangayar nazarin kula da filaye da gine-gine a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, Bioye Tajudeen Aluko ya kwatanta gwamnonin Najeriya a matsayin masu kwace filaye, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin jawabi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a wani taro na kara wa juna sani, Aluko ya ce suna boyewa karkashin dokokin filaye wurin mallakar filaye da kuma mallaka wa mutanensu.

Read also

Abin da ya sa Gwamnati ba ta isa ta rabawa Talakawa kudi idan an cire tallafi ba - ‘Yan Majalisa

Wani Farfesan Najeriya Ya Kira Gwamnoni 'Masu Kwacen Filaye'
Farfesan Aluko Ya Kira Gwamnoni 'Masu Kwacen Filaye'. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto cewa Farfesan, wanda shine bako mai jawabi a taron ya ce gwamnoni su na da dabi’ar azurta kawunansu da abokan siyasarsu da filayen jama’a.

A cewarsa, gwamnoni suna mayar da harkokin filaye a karkashin ikonsu, inda yace yana mamakin yadda gwamnan da ya dace ya mayar da hankali akan ci gaban jiharsa ya ke da lokacin kwallafa rai a filaye.

Aluko ya bukaci a cire dokar filaye daga kundin tsarin mulki

Aluko ya yi suka akan dokar filaye, ya kuma bukaci a cireta daga kundin tsarin mulkin Najeriya.

A cewarsa ya kamata a kara gyara sabuwar dokar filaye, inda ya bukaci a ba mai fili na asali abinsa don kawo karshen rigima.

Ya kara da cewa:

“Sashi na daya a dokar filaye bai cire asalin mai fili a matsayin mai fili ba. Sai dai masu kwacen filaye da suke boyewa a karkashin dokar.

Read also

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

“Asalin mai fili shi ne mai fili ba masu boyewa karkashin doka ba. Shiyasa kake ganin gwamnoni su na azurta abokansa a matsayin kara ta siyasa.
"Idan kai ba dan jam’iyyarsu bane ba za ka taba samu fili ba. Hakan kwacen fili ne, ko wanne suna zaka kira dabi’ar da shi ka kira, amma kwacen fili ne.”

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Read also

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel