Ga dalili da ya sa aka kasa sayar da gidajen Kwankwasiyya
- Har yanzu dai mutane ba su shiga rukunin gidajen Kwankwasiyya ‘City’
- Babu yadda za'a yi mai ƙaramin ƙarfi ya mallaki gida na miliyan 27
- Gwamnatin Ganduje dai ta ce ta gagara sayar da gidajen ne
- Wasu masana sun ce kamata ya yi a bada hayan gidajen da ba'a sayar ba
A Najeriya, yayin da ƙananan ma`aikata da sauran masu ƙaramin ƙarfi ke neman hanyar mallakar muhalli ido-rufe, wasu gidajen da gwamnati jihar Kano ta gina sun kama hanyar yin kwantai.
Har yanzu dai mutane ba su shiga rukunin gidajen Kwankwasiyya ‘City’ da Amana ‘City’ da kuma Bandirawo ‘City’ ba, wadanda gwamnatin Engineer Rabiu Musa Kwankwaso ta gina.
KU KARANTA: Daukar sabbin matakai kan sarkin Kano ba dai-dai bane - Inji Bafarawa
Wani mai ƙaramin ƙarfi a jihar, Haruna Ado Umar ya ce ya kan ji matukar taikaci idan ya ga gidajen babu kowa a ciki.
'Babu yadda za'a yi mai ƙaramin ƙarfi ya mallaki gida na miliyan 27', in ji shi.
Yadda Legit.ng ya samu labari, gwamnatin Ganduje dai ta ce ta gagara sayar da gidajen ne saboda masu ƙaramin ƙarfi na kukan cewa sun yi matukar tsada.
KU KARANTA: Kasan yawana ýan Najeriya da ‘Cutar daji’ ke hallakawa a duk rana?
Ta kara da cewa tuni da dukufa wajen gina wasu sabbin gidaje masu daki uku-uku da ake sayar da su akan Naira miliyan 2.850 wadanda masu ƙaramin ƙarfin zasu iya saye.
Sai dai wasu masana sun ce kamata ya yi a bada hayan gidajen da ba'a sayar ba kasancewar sun yi tsada ga masu son saye.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wannan Legit.ng bidiyo ya nuna yara suna roko kar gwamnati ta rushe musu gida
Asali: Legit.ng