Matashi Gaddafi Ya Hallaka Kishiyar Mamarsa Da Juna Biyu Kuma Ya Kashe Diyarta a Kano

Matashi Gaddafi Ya Hallaka Kishiyar Mamarsa Da Juna Biyu Kuma Ya Kashe Diyarta a Kano

  • Wani yaro ya kashe amaryar maihaifinsa mai dauke da ciki kuma ya kashe diyarta a Kanon Dabo
  • Jami'an hukumar yan sanda sun damke shi a wani kango yayinda yake kokarin gudu daga jihar
  • Yaron dan shekara 20 kacal ya yi bayanin dalilin da ya sa ya hallaka matar da kuma yarinyar

Kano - Wani Matashi dan shekara 20 ya shiga hannun hukuma kan zargin aikata laifin kisa a Fadama Rijiyar Zaki Quarters, karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano.

Hukumar yan sanda ta bayyana cewa matashin mai sun Gaddafi Sagir ya kashe kishiyar mahaifiyarsa mai juna biyu, Rabiatu Sagir tare da diyarta, Munawwara Sagir.

An tattaro cewa Gaddafi ya yi wannan aika-aika ne kan cewa kishiyar ce tayi silar rabuwar mahaifinsa da mahaifiyarsa.

Saboda haka ya yanke shawarar dauka 'danyen hukunci a kanta. Yayinda kuma diyarta ta ganshi yana kashe mata mahaifiya, ita ma ya hada da ita.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

Gadsafp
Matashi Gaddafi Ya Hallaka Kishiyar Mamarsa Da Juna Biyu Kuma Ya Kashe Diyarta a Kano Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da labarin ya bayyana cewa tuni an damke Gaddafi yayinda yake kokarin guduwa daga jihar, rahoton Vanguard.

Yace Gaddafi ya amsa laifin da ake zarginsa da shi kuma yace shi kadai ya aikata.

Kiyawa yace:

"A ranar Asabar misalin karfe 11:30 na dare aka samu rahoto daga wajen Sagir Yakubu wanda yace ya dawo gida ya tarar da gawar matarsa mai ciki, Rabiatu Sagir (25) da diyarta Munawwara (8) kuam yana zargin 'dansa Gaddafi."
"Yayin samun rahoton kwamishanan yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya bada umurni ga jami'ai karkashin CSP Usman Abdullahi, DPO na Rijiyar Zaki su garzaya wajen, su kai matan asibtii kuma su damke wanda yayi kisan."
"Kai tsaye jami'an suka dira wajen, kuma suka kaisu asibiti inda Likita ya tabbatar da cewa sun mutu."

Kara karanta wannan

Ko Tinubu Yana Taba Kirifto Ne: Yasha Alwashin Taimakon Yan Kirifto In Ya Kai Ga Gaci

"An damke wanda ake zargin, Gaddafi Sagir, dan shekara 20 a cikin wani gida yana kokarin guduwa daga Kano."
"Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin cewa shi kadai ya aikata laifin da Skun Direba, ya cakawa amaryar babansa a wuya da goshi kuma ya shake diyarta har lahira."

Asali: Legit.ng

Online view pixel