Tsadar Kudin Wuta: Tinubu Zai Dawo Aiki da Sola, An Ware N10bn a Fadar Aso Villa
- An ware N10bn a kasafin kudin 2025 domin samar da na’urar wuta mai aiki da hasken rana a fadar shugaban kasa
- Samar da wutar sola zai rage dogaro da lantarki a fadar shugaban kasa da kuma rage matsalar tsadar kudin shan wuta
- An ruwaito cewa a shekarar 2024 kawai, fadar shugaban kasa ta kashe sama da N483m wajen biyan kudin lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da ware zunzurutun kudi N10bn a cikin kasafin kudin 2025 domin samar da wutar sola a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, Abuja.
Matakin na zuwa ne yayin da ake kara fuskantar matsalolin rashin wutar lantarki da kuma hauhawar kudin wuta a fadin kasar nan.

Asali: Getty Images
Rahoton da jaridar Punch ta fitar ya bayyana cewa karin kudi a kasafin fadar shugaban kasa daga N47.11bn zuwa N57.11bn ya samo asali ne saboda samar da wutar sola da ake shirin yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin zai taimaka wajen takaita kashe kudin lantarki da gwamnati ke yi, musamman duba da cewa kudin lantarki ga masu amfani da layin Band A ya tashi tun shekarar 2024.
Kudin wuta ya jefa Aso Villa cikin bashi
A Fabrairun 2024, kamfanin AEDC ya bayyana fadar shugaban kasa a matsayin daya daga cikin manyan wadanda ake bi bashi, inda aka bayyana AEDC na bin Aso Rock bashin N923.87m.
Sai dai bayan sake dubawa, an rage wannan bashi zuwa N342.35m, kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a biya kudin nan take don kauce wa yanke wutar.
An gano cewa fadar shugaban kasa ta kashe N483.34m wajen biyan kudin wuta a 2024, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 40.17 idan aka kwatanta da N344.82m da aka kashe a 2023.
Gwamnati na sa ran rage kashe kudi a 2025
A kasafin 2025 da aka amince da shi, an ware N311.09m ne kawai domin biyan kudin lantarki na fadar shugaban kasa.
Adadin ya yi kasa idan aka kwatanta da abin da aka kashe a shekarar da ta gabata, lamarin da ke nuna kokarin rage yawan kashe kudi ko kuma hasashen za a samu raguwar bashin.
Sai dai, wasu na ganin wannan adadi na iya kasa da bukatun Villa idan aka duba yadda aka rika tara bashi a shekarun baya.

Asali: Getty Images
Baya ga aikin sola, gwamnatin tarayya ta ware N11.92bn domin biyan bashin da Julius Berger da wasu kamfanonin ke bin ta tun daga shekarar 2022.
Haka kuma, an ware N6.04bn domin gyare-gyaren shekara-shekara na na’urori da gine-gine da ke fadar shugaban kasa.
Tinubu zai gana da hafsoshin tsaro a Villa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa.
Bola Tinubu ya dauki matakin ne domin kokarin kawo zaman lafiya a yankuna daban daban na kasar nan.
Tun bayan tafiyar shugaban kasa kasashen Turai aka samu kashe kashe a wasu jihohi da ake cewa an kashe mutane akalla 120.
Asali: Legit.ng