'Ku Sauya Sana'a': Ɗan Majalisa a Kano ya Fadawa Mafarauta Gaskiya kan Zuwa Kudu

'Ku Sauya Sana'a': Ɗan Majalisa a Kano ya Fadawa Mafarauta Gaskiya kan Zuwa Kudu

  • 'Dan majalisar tarayya, Alhassan Kabiru Rurum, ya shawarci jama’arsa su daina farauta a Kudu saboda matsalolin tsaro da ke kara kamari
  • Ya ce lamarin da ya faru a Edo inda 'yan farauta 16 suka mutu ya nuna cewa yin farauta a jejin da ke Kudancin Najeriya ba shi da amfani
  • Rurum mai wakiltar Rano da Bunkure ya ce ba za ka dauki bindiga da adda ka shiga unguwa ba tare da fahimtar yare da al'adunsu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Rano da Bunkure, Hon. Alhassan Kabiru Rurum, ya shawarci yan yankinsa kan farauta a Kudu.

Hon. Rurum ya bukaci jama’ar yankinsa su daina farauta a Kudancin Najeriya saboda rashin tsaro.

Dan majalisa ya shawarci matasa kan zuwa farauta a Kano
Hon. Alhassan Kabiru Rurum ya gargadi matasa kan zuwa farauta Kudu. Hoto: Nazifi Jarumi Rurum.
Asali: Facebook

Rurum ya shawarci matasa kan farauta a Kudu

Ɗan majalisar ya fadi haka yayin da ya kai ziyara yankin a yau Alhamis 17 ga watan Afrilun 2025 a kauyen Bunkure, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rurum ya ce wannan dabi’a ba ta da amfani yanzu duba da yadda matsalar tsaro ke ta kara kamari a kasar.

A cewarsa:

“Mutanemu su daina wannan dabi’a, su duba halin da ake ciki yanzu, lamarin ya tabarbare kwarai."

Ya ce abubuwa sun canza sosai, kuma saboda matsalolin tsaro da ke ko’ina, wasu al’adu dole su tsaya.

Ya kara da cewa:

“A wannan zamani, ba za ka iya daukar bindiga da adda ka shiga Kudu da sunan farauta ba, abubuwa sun sauya.
“Ina so ku duba kamar wani daga Kudu ya zo nan dauke da makamai, ba ku fahimci yarensa ba, da me za ku ji.
“Haka ma ba za ka shiga Kudancin kasa da makamai kana cewa farauta kake yi ba, al’ada da harshe ma ba ku fahimta ba.”

Dan majalisa ya fadawa matasan Kano gaskiya kan zuwa farauta Kano
Hon. Alhassan Kabiru Rurum ya gargadi matasan Kano kan barin gida zuwa farauta Kudu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Hon. Rurum ya ba iyalan mafarauta tallafi

Hon. Rurum ya ce abubuwa da dama sun sauya ba kamar yadda aka sani a baya ba inda ya ce wannan ba dabi'a ba ce mai kyau.

“Abubuwa sun canza a kasar nan, ba kamar da ba, saboda haka muna kira gare su da su dakatar da wannan dabi’a.
“Za mu gana da kungiyoyin masu farauta a jihar don tabbatar da an dakatar da irin wannan dabi’ar gaba daya.”
“Muna rokonku da ku dakatar da irin wannan aiki ku zauna ku yi tunani ku fitar da wata hanya mai sauki da zaman lafiya.”

- Cewar Hon. Rurum

Ya kuma ba da tallafin N5m ga iyalan wadanda suka mutu, tare da alkawarin gina makaranta domin tunawa da su.

'Yan sanda sun kama mafarauta a Edo

Kun ji cewa ‘yan sanda ta Edo ta ce an cafke mafarauta hudu daga Kano da makamai yayin da suka isa jihar da dare.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa an kama mafarauta ne ba Fulani makiyaya ba.

Sunayen mafarautan da aka kama sun hada da Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris, da Jamilu Habibukuma daga Doguwa a jihar Kano suka fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.