Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)

Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)

A kan samu matsala a bangaren sanya kaya na manyan mutane amma wannan zai iya zama na daban ne. Ganin bayyanar shugaban kasa a taron manyan jami'an gwamnati da takalmi mai matukar kura ba zai yiwa 'yan kasa dadi ba. Hakazalika masoyan shugaban kasan zasu nuna tsananin damuwarsu.

Ta shafin fadar shugaban kasar na tuwita ne aka tabbatar cewa shugabannin kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta ziyarceshi, kuma aka wallafa hotunan shugaban kasan tare dasu yana gaisawa.

Wadanda suka ga wannnan hoto sun kasa hakuri har sai da suka dinga yin wasu tambayoyi a kan dalilin ganin takalman shugaba Buhari sun yi futu-futu da kura.

Ba a kan masu lura da kayan shugaban kasan bane kawai mutane suka dinga dora laifi ba, har da masu daukar hotunan nashi da suka dauki wadannan takalman duk da kura a jikinsu. Ta yaya zasu tozarta shugaban kasa haka? Wasu kuma mamaki suke yi a kan a ina aka samu kura a fadar shugaban kasa?

Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)
Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)
Asali: Instagram

Idan bamu manta ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis, 9 ga watan Janairu, ya fada ma mambobin kungiyar malaman jami’a (ASUU) da su bayar da hadin kai a manufar yaki da rashawar gwamnati ta hanyar amincewa da manufofin dake dabaibaye da tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun sace matafiya 7 a daf da Maiduguri

Hakan ya kasance sakamakon ganawarsa da shugabannin kungiyar malaman a ranar Alhamis, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. An tattaro cewa kungiyar ta ASUU na adawa da yiwa mambobinta rijista kan tsarin IPPIS.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana IPPIS a matsayin kutse wanda ya saba ma yarjejeniyar da ke tsakanin kungiyar da gwamnati.

Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)
Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)
Asali: Twitter

Sai dai shugaba Buhari a wani jawabi daga hadiminsa, Femi Adesina, ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali sosai wajen inganta jami’ai da tsarin makarantun jami’a ta yadda za a dunga yaye dalibai masu inganci, kamar yadda ya ba da tabbacinn cewa daga yanzu za a ba ilimi kula na musamman a kokarin inganta kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel